Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya bukaci kafafen yada labarai da su yi watsi da masu kiraye-kirayen da zai haifar da rashin hadin kai, su kuma baiwa masu kokarin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai muhimmanci.
IBB ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya a gidansa da ke Minna, Jihar Neja.
IBB, ya ce dole ne ‘yan Nijeriya su dage wajen yin imani da hadin kan Nijeriya tare da rokonsu da su yi hakuri tare da yin addu’a wurin shawo kan kalubalen da ke addabar kasar.
Tsohon shugaban kasar, ya nuna jin dadinsa kan rawar da kafafen yada labaran Nijeriya ke takawa, ya kuma yi kira da a sauya tunanin domin samar da ingantacciyar Nijeriya ta hanyar yin abin da ya dace.
Dattijon ya kuma yabawa masu aikin yada labarai a kasar nan kan yadda suke gudanar da aikinsu cikin kwarewa da goyon bayan da suke ba dimokuradiyya wurin dorewarta.
Tsohon shugaban kasar ya roki ‘yan Nijeriya da su kasance masu jajircewa, rikon amana da addu’a domin kawo karshen kalubalen rashin tsaro da al’umar Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Tsohon shugaban kasan yana wannan bayani ne a dai dai lokacin da ake jajiberin zaben 2023.
Source:leadershiphausa