Ministar Jinkai, Hajiya Sadiya Umar Farouk ta bayyana cewa idan hukumomi za su mike tsaye wajen hukunta masu safarar yara zuwa wuraren aikatau za a samar da zaman lafiya mai dorewa.
Hajiya Sadiya Umar Farouk ta bayyana haka ne a gagarumin bikin tunawa da ranar safarar yara wanda Majalisar Dinkin Duniya ta shirya domin tausaya wa ga kananan yarar da ake safararsu zuwa wasu kasashe.
Ta yi kira ga hukumomin Nijeriya da su dauki kwararen mataki wajen hukunta duk wanda aka kama da safarar yara zuwa bautar da su da niyyar samun kudade walau a Nijeriya ko zuwa kasar waje, wanda ake bautar da su ko sanya su harkokin karuwanci da aikatau da makamancinsu.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya (UNODC) tare da hadin gwiwar kungiyoyi masu yaki da safarar mutane da kuma hukumar da ke yaki da safarar mutane (NAPTIP) sun shirya wani taro domin wayar da kan al’umma ta yadda za su zage dantse wajen yaki da masu safarar yara.
Masu jawabi dabam dabam sun bayyana illolin da ake samu a irin wannan mummunar sana’a. sun ce safarar mutane ba karamin ta’addanci ba ne kuma take hakkin Dan’adam ne.
Duk shekara dubban maza da mata da yara kananan ke fadawa cikin wannan mummunan sana’a na safarar mutane, kuma abin takaici ba’a hukunta masu sanya su cikin wannan sana’a.
Duk da kiraye-kiraye da ake yi da yunkuri na shawo kan matsalar, Nijeriya tana daga cikin kasashe wanda ake amfani da safarar mutane don lalata rayuwar mutane. Idan aka samu aka shanyo kan matsalar, tabbas za a samu sauki sosai kuma zai kange mutane da dama daga kamuwa da cututtuka.