Jaridar Phompenh Post tya bayar da rahoton cewa, hukumomin soji a kasar Myanmar sun saki malamin addinin buda mai tsananin kin musulmi Ashin Wirathu da ake tsare da shi a gidan kason kasar.
Hukumomin da suka shude ne dai suka kame Ashin Wirathu ne an tsare shi a gidan kaso, bisa zarginsa da tunzura jama’a da kuma yin abubuwan da za su iya haifar da tashin hankali.
Gwamnatin da sojoji suka hambarar a kasar Myanmar ce dai ta kame shi ta jefa shi kurkuku, bayan ya shiga wata zanga-zangar adawa da gwamnati.
Kafin wannan lokacin dai a cikin shekara ta 2017 jagoran mabiya addinin buda a kasar Myanmar ya bayar da umarnin Ashin Wirathu gudanar da duk wasu harkoki na addini a wuraren ibada na ‘yan addinin buda, saboda yadda yake tunzura jama’a wajen kin jinin musulmi a kasar.
A wani labarin kuma yau ne kwamitin da ke kula da shirya tarukan makon hadin kan musulmi na duniya ya fara gudanar da zamansa tare da halartar dukkanin mambobi.
Shugaban kwamitin Mahdi Agha Muhammad ne ya sanar da hakan a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, inda ya bayyana cewa, zaman taron na farko da aka fara an tattauna yadda zaman zai kasance a wannan shekara.
A shekarar bara saboda matsalolin da ake ciki na bullar cutar korona, an gudanar da taron ne kai tsaye ta hanyar hotunan bidiyo na yanar gizo, inda masu gabatar da jawabai suka rika gabatar da jawansu da makaloli kai tsaye.
Ya ce har yanzu wanann batu yana daga cikin abin da yke ci wa al’ummomin duniya tuwo a kwarya, a kan haka sun fara tattaunawa kan yadda taron na bana ya kamata ya kasance, duk kuwa da cewa ba a yanke shawara guda kan hakan ba, amma za a ci gaba da tatatunawa domin samun matsaya guda.
Kwatin da ke daukar nauyin shirya tarukan hadin kan musulmi na duniya dai yana karkashin cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya ne, da ke da babban ofishinta a birnin Tehran.
Marigayi Imam Khomenei ne ya kirkiro makon hadin kan musulmi musulmin duniya, wanda ya sanya makon haihuwar manzon Allah a cikin watan watan rabi’ul Awwal ya zama shi ne makon hadin kan musulmi na duniya baki daya.