Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wasu mutane 85 da take zargi da ta’ammuli da miyagun kwayoyi a wani gidan casun dare da ke Kano a ranar Litinin.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kano, Abubakar Idris-Ahmad, kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar, ya ce kamen ya biyo bayan korafe-korafen da aka kai kan yawaitar masu ta’ammuli da miyagun kwayoyi a gidan casun.
Ya ce, masu gidan casun ne suka shigar da korafe-korafen ga hukumar kan yadda aka mayar da gidan wurin shan miyagun kwayoyi.
Ya kara da cewa, wadanda aka cafken sun hada da maza 55 da mata 30, daga cikin kwayoyin da aka kama a tare da su akwai tabar wiwi da sauran kwayoyi.
Mista Idris-Ahmad ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton ayyukan da suka shafi ta’ammuli da muggan kwayoyi ga hukumar domin hukumar ba za ta bar wata maboyar masu safarar miyagun kwayoyi a jihar ba.
A wani labarin dag Bauchi kotun Majistire mai lamba ta daya da ke Bauchi ta amince da bukatar bayar da belin Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi bisa sharadin guda uku.
Idan za a tuna dai, ‘yansandan sun gurfanar da Malamin ne a gaban kotun bisa zarginsa da tada zaune tsaye da ka iya barazana ga zaman lafiyan jama’a. Kuma hakan ya biyo bayan korafin da kungiyar Fitiyanul Islam ta shigar ne a kansa.
Da ya ke yanke hukunci kan bukatar belin, Mai Shari’a Abdulfata Baba Shakoni, ya ce, ya amince da bukatar belin malamin bisa sharadi guda uku, na farko zai kawo Hakimi, na biyu Babban Sakatare da ke aiki a karkashin Gwamnatin jihar Bauchi da kuma wani Malami da ke kwayan Bauchi.
Kazalika, ofishin Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a ta jihar Bauchi sun bukaci kotun da ta amince musu su amshi ragamar karar daga hannun ‘yansanda domin cigaba da Shari’ar.
Daga bisani kotun ta amince da wannan bukatar.
Da ya ke karin haske kan hukuncin, daya daga cikin lauyoyin da suke kare malamin, Barista Sadik Abubakar Ilelah, ya nuna farin cikinsu bisa samun belin malamin tare da cewa insha Allahu za su cika sharudan da Alkalin ya gindaya.
Da yake bayani kan amsar ragamar karar da suka yi, daya daga cikin lauyoyin a ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi, Aliyu Ibn Idris, ya ce, “Shi Antoni Janar na jiya ko na tarayya yana da dama da dalili ba dalili ya shiga cikin kara.”
“Antoni Janar ya shigo ya karbi Kes ba sabon abu ba ne. Iyakaci abun da za a duba shigowar tamu za ta haifar da adalci ko ba za ta haifar da adalci ba. Insha Allahu za mu yi iyaka abun da za mu yi a wanzan da adalci a kai,” Inji shi.
Sannan, ma’aikatan shari’an ta bukaci ‘yanda da su ba su kundin Shari’ar da sauran abubuwan da suka hada wajen shigar da cajin domin nazarin akwai bukatar canzawa ko a’a.
Daga bisani dai Alkalin ya dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan nan da muke ciki domin cigaba da shari’a.
Wakilinmu ya labarto cewa an sake komawa da malamin zuwa gidan yari har zuwa lokacin da za su cika sharadin belin.