Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano, ta ce ta ceto mutane 12 da kadarori da kudinsu ya kai Naira miliyan 130 daga gobara 78 da suka faru a watan Maris a jihar.
Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ne, ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), a ranar Laraba a Kano.
Abdullahi, ya kuma ce mutane 10 ne suka mutu, yayin da gobarar da ta lalata kadarorin Naira miliyan 71.
“Mun samu kiran agaji 27 da wayar karya 11 daga mazauna jihar a tsawon watan Maris,” in ji shi.
Ya shawarci jama’a da su kasance masu kula da abubuwan da suka shafi wuta.
A wani labarin na daban gwamnatin Tarayya ta sanar da karin kudin wutar lantarki da ‘yan Nijeriya ke biya, wanda hakan ya haifar da cece-kuce a tsakanin mutane.
Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya (NERC), ta yi karin kashi 240 cikin 100 na kudin wutar lantarki da ‘yan Nijeriya ke biya, inda ta ce hakan zai ba ta damar biyan kudin gas da kuma sauran gyare-gyaren injina da suka shafi rarraba wutar lantarki.
LEADERSHIP ta yi duba kan yadda sabon tsarin biyan kudin wutar lantarki zai kasance da kuma mutanen da ya shafa.
NERC ta kara farashin kudin wutar lantarkin kan Naira 225 kan kowane kilowat a awa daya, amma wannan kari zai shafi iya wadanda suke kan rukunin samun wuta na ‘A’ ne kadai.
Hukuncin dai na zuwa ne, daidai lokacin da ake fama da matsalar rashin wutar lantarki a fadin kasar nan.
Ga yadda tsarin biyan kudin wutar lantarkin zai kasance:
1.NERC ta amince da karin farashin wutar lantarki da kashi 240 ga kwastomomin da ke rukunin ‘A’, wanda kudin ya tashi daga Naira 66 zuwa Naira 225 a kowace awa daya.
2. Wannan karin ya shafi kwastomomin da ke samun wutar lantarki na awa 20 ko sama da haka, wadanda ke kan hanyoyin samar da wuta 481 daga 3,000, wanda ke wakiltar kashi 15 na mutanen da ke amfani da wutar lantarki a Nijeriya.
3. Masu amfani da wutar lantarkin da ba sa samun wutar awa 20 a rana, dole NERC za ta rage yawan abin da za su ke biya tare da sauya musu rukuni.
4. Wadanda suke kan rukunin ‘A’ za su fuskanci gagarumin karin farashin kudin wutar lantarki wanda zai iya tashi daga N50,000 zuwa N170,000 duk wata, amma ya danganta da yadda suka yi amfani da lantarkin.
5. Kwastomomin da ke kan rukunin ‘A’ ne kadai ke da tabbacin samun wutar lantarkin akalla awa 20 daga kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11, kamar yadda NERC ta bayyana.
6. Kwastomomin da ke kan rukunin ‘B’, ‘C’, ‘D’, da ‘E’, wadanda ke samun wutar lantarkin kasa da awa 20, karin kudin ba zai shafe su ba.
7. Karin kashi 240 na nufin gwamnati ta cire tallafin wutar lantarki gaba daya a kan kwastomomin da ke rukunin ‘A’, wadanda ke wakiltar kashi 15 na masu amfani da wutar lantarki, sannan kashi 40 na wutar lantarkin da ake rarrabawa a fadin kasar nan.
8. An kaddamar da karin ne a ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu, 2024, wanda ke nufin kwastomomin rukunin ‘A’ ne kadai karin kashin 240 na wutar lantarki zai shafa.
9. Duk da karin kudin wutar lantarkin da aka yi, amma kwastomomi na fuskantar koma baya na samun wuta tun daga watan Janairu 2024, wanda ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya danganta lamarin da karancin gas da ake fama da shi a kasar nan.
Sai dai wannan kari na kudin wutar lantarki da gwamnati ta yi, zai ta’allaka ne gaba daya da wutar da kwastomomi ke samu a rana, wanda da shi ne kadai za a yi alkalacin abin da za su biya duk wata.
DUBA NAN: Dan Nasiru El- Rufa’i Ya Maida Martani Ga Gwamna Uba Sani
10. Wadanda suke kan rukunin ‘A’ za a iya dawo da su wani rukunin matukar ba sa samun wutar lantarkin awa 20 a kowace rana.