Hukumar dake shirya jarabawar share fagen shiga jami’a ta JAMB ta karyata wani labari da aka yada dandane da cewa zata shirya sabon lokacin gudanar da jarabawa ga wasu dalibai.
Hukumar a ta bakin mai magana da yawun ta mista Benjamin ta tabbatar da cewa labarin bashi da maraba da kanzon kurege wanda bashi da mkama balle tushe.
A tattaunawa da manema labarai a birinin lagos mista benjamin ya tabbatar da rashin sahihancin labarin inda yake labarin wasu ne suka yada shi amma baya da tushe a ta bakin sa.
Sanarwar da aka fitar a ranar labara ta kawo karshen fatan da wasu daga cikin daliban suke dashi sakamakon samun wancan labari.
Dalibai da dama sun fadi jarabawar ta share fagen shiga jami’a wanda hakan ya zama babban dalilin da zai hana su shiga jami’a a wannan shekarar ta 2021.
An kiyasata kusan kaso saba’in cikin dari na daliban da suka zana jarabawar basu samu sakamakon da hukumar ta samar domin shallake shingen dake tsakanin su da zama ‘yan jami’a ba.
Lamurran ilimi dai na fuskantar babbar barazana a najeriya, kama da matsalar masu satar dalibai da suka yawaita a arewacin najeriya gami da lalacewar tsarin bada ilimi a kasar.
Wasu daga cikin iyayen yaran da suka fadi a jarabawar ta share fagen shiga jami’a sun koka sosai inda suka nuna sun kashe kudi masu yawan gaske kafin suyi ma ‘ya’yan su rijista amma abin takaici yanzu anzo ance ‘ya’ayan su sun fadi jarabawar, yanzu kuma basu san yadda zasuyi da ‘ya’yan su ba.
Ga mafi yawancin dalibai dai sukan kwammace su shiga wasu makarantun irin su polytechnic, fce ko kuma legal domin samun sauki duba da manyan matsalolin dake tattare da kokarin samun gurbi a daya daga cikin jami’oin kasar.
Ana iya cewa zama dan jami’a dai ya zamewa wasu daga cikin dalibai hangen dala.