Hukumar Yaki da halarta kudaden haramun ta kasashen Afirka ta Yamma GIABA ta fara wani taron horar da manyan jami’an tsaron dake aiki akan iyakokin Najeriya akan yadda zasu dakile safarar haramtattun kudade ta kan iyakokin kasar wadanda ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci.
Daraktan yada labaran GIABA Timothy Melaye ya bayyana muhimmacin daukar matakai domin dakile yadda ake safarar kudaden haramun wadanda bata gari ke amfani da su wajen sayen makamai da kuma kwayoyin da suke kaiwa hannun Yan ta’adda.
Melaye yace sun dauko kwararru daga sassa daban daban domin karawa jami’an tsaron sani dangane da yadda zasu inganta ayyukan su wajen hana safarar kudaden musamman ganin yadda Najeriya ke fuskantar matsalar ayyukan ta’addanci.
Wakilin shugaban hukumar kwastam ta kasa, Kanar Hammeed Ali yace babu wata hukumar tsaro da zata iya wannan aikin ita kadai ba tare da hadin kai da sauran hukumomi ba.
Jami’in yace wannan na daga cikin abinda ya baiwa hukumar kwastam nasarar kama haramtattun kayayyakin da aka shiga da su Najeriya a watannin da suka gabata.
Mrs Biola Shotunde, Daraktar binciken asiri na rundunar Yan Sandan dake yaki da halarta kudaden haramun tace Najeriya na bada hadin kai sosai wajen wannan yakin da kuma hadin kai tare da wasu hukumomi irin na su a kasashen duniya wajen ganin an samu nasarar dakile safarar kudaden haramun.