Matashiya ‘yar Nijeriya, Hilda Bassey Effiong da aka fi sani da Hilda Baci, ta zama sarauniyar dafa abinci ta duniya bayan da ta shiga gasar dafa abinci mafi tsawo wacce ta shafe kusan awa 100 tana dafe-dafen abinci kala-kala.
Hakan ya biyo bayan wani gasa ne da Guinness ta shirya ga duk wani ko wata da zai ko ta yi girki mafi tsawon lokaci ba tare da dakatawa ba.
Baci wacce ‘yar kasar Nijeriya ce mai shekara 27 a duniya, an haifeta ne a karamar hukumar Nsit Ubium da ke jihar Akwa Ibom, ta yi girki na tsawon sama da kwanaki hudu ba tare da zaunawa ba, inda ta dafa abinci kala-kala har sama da dari tare da rabar wa mutane kyauta.
Taken shiga gasar ta duniya shi ne ‘Dafa abinci cikin Kayyadadjen lokaci’. Ta fara girkin ne a ranar Alhamis makon jiya ta kammala ranar Litinin 15 ga Mayu, 2023 da yamma.
‘Yar Nijeriya da ta kafa tarihin nan a bangaren girki, Hilda Bassey Effiong, da aka fi sani da Hilda Baci, ta yi bayanin irin gwagwarmayar da ta sha wajen shiga a dama da ita da har ta samu nasara a bangaren dafa abinci wacce ta shafe tsawon awanni 100 tana girki.
Baci ta kammala karatunta ne a sashin nazarin ilimin zamantakewa daga jami’ar Madonna wacce ta fito daga gasar dafa abinci na tsawon awa 100, ta gode wa Allah da ya taimaketa ta cimma wannan nasarar da iyayenta da ‘yan uwanta.
Ta ce, ana gaf da karaya bayan shiga gasar, sannan, ta karar da dukkanin kuzarin jikinta da zai ba ta karfin guiwar cigaba, amma duk da hakan ta jure ta cigaba har sai da ta cimma nasara.
Ta ce, “Ina matukar godiya wa Allah. Na kusa sarewa a wannan gasar sa’o’i shida bayan da na fara a ranar Alhamis (Makon jiya), don na gaji kuma ba zan iya cigaba ba, amma mahaifiyata ta karfafeni ta kara min kumaji domin ta tsaya a tare da ni na tsawon awanni 14 hakan ya karfafa min guiwa matuka.
Ina kan wannan matakin nasarar ne saboda goyon bayanku da na mahaifiyata.
“Ina son na shaida muku dukkaninku cewa kowani irin mafarki na iya zama gaskiya, na shirya wannan samun wannan nasarar tun shekaru biyar da suka gabata, hakan ya zama cikin mafarkina, amma ban iya yin hakan wancan lokacin ba, amma yau ga shi na iya yi dukka saboda ku.
Ku nace kan mafarkinku wata rana zai zama gaskiya.”
Hilda Baci ‘My Food My Hilda’ ta lashe gasar dafa abinci na Guinness Book of Records, da ta shiga fagen dafa abinci na tsawon awa 100, lamarin da ya bai wa jama’a da dama mamaki matuka da farkar da dumbin matasa.
Masu kallon wannan al’amarin na ban mamaki da sha’awa na gasar abinci wanda aka nada a faifayin dauka, sun nuna bajintar Hilda a matsayin abun mamaki matuka gaya.
Hilda mai shekara 27, yanzu ta kafa babban tarihin wacce ta fi kowa jimawa a fagen dafa abinci.
Da take shelanta nasarar Baci na dafa abinci na tsawon awannni 96 zuwa 100 zuwa ranar Litinin din da ta gabata, babbar kawarta ta wallafa a shafin Instagram @ama_reginald cewa, “Baci ta kusan kaiwa awa 100 tana girki.”
Zuwa ranar Litnin da karfe 7:00pm, Baci ta kai awanni 99 a dakin dafa abinci, lamarin da ya kaita kwace ragamar wannan kambun a hannun wata ‘yar kasar India, Lata Tondon da ta zama tauraruwar dafa abinci na duniya a shekarar 2019.
Tata Tondon ‘yar kasar Indiya ce take rike da kambun bayan da ta shafe sa’o’i 87 da mintuna 45 a shekarar 2019 tana girki.
Masu shirya gasar ‘Guiness World Record’ sun ce, kafin su amince da mutum ya samu nasarar sai ya gabatar musu da kwararan hujjojin lashe gasar da dukkanin matakan da aka gindaya.
Daga cikin abubuwan da ake alakari da su shine na farko mai bukatar shiga gasar zai gabatar da bukatar nuna sha’awar hakan da gabatar da kansa, zai/za ta yi girki na tsawon kwanaki 4 ba tsayawa; dole mai shiga gasar ya yi girki mafi tsawo ba tare da zaunawa ba, wanda ya fi yin girki na tsawon lokaci bai sare ba shine ke da kambun.
Kazalika, babu shan wasu kwayoyin kara kuzari ko na karfin jiki yayin shiga gasar ba; mai shiga gasar na da damar cin abinci, shan ruwa ko ruwan ‘ya’yan itace, da shan glucose.
Ita dai Baci ta shiga gasar ne daga wurin shakatawa na ‘Amore Gardens’ da ke Lekki, Jihar Legas, Nijeriya. ta yi girki safe da dare da rana na tsawon darare 4 ba tare da yin barci ba. Ta kan samu hutun minti 5 a kowani awa.
Ta na kwashe mintuna 30 a cikin motar asibiti da ke kusa da ita, inda za ta iya yin barci, ta yi amfani da dakin wanka, sannan ta sami tantancewar likita ko duba lafiyar ta daga tawagar likitoci.
Kazalika, duk abin da ta dafa tana raba wa mutanen da ke wurin kyauta ba tare da sayar da abincin ba. Ta kan dafa abinci daban-daban lokaci guda.
Tana da ‘yancin dafa duk abincin da take so. Babu takurawa kan girkin da ta iya da wanda ba ta iya ba.
Kowane abinci da aka dafa da kowane farantin da aka ba da shi ana rubuta shi. Ta dafa abinci sama da kala 115 kawo yanzu.
Kuma dukkanin yadda mai shiga gasar ya kasance to zai tura kai tsaye wa masu kula da gasar don haka ne ta kafa wannan tarihin.
Sai dai, masu shirya gasar sun ce, bayan mutum ya tura musu daukan hujjojinsa, to za su shafe tsawon mako 12 suna bibiya da tantance abubuwan da aka turo musu kafin daga bisani su amince da shi ko kin amincewa da shi.
- Ta Kasance Jaruma, Mai Aiki Tukuru – Cewar Ahlinta
Iyalanta da makusantansa tauraruwar girki ‘yar Nijeriya, Hida Baci, sun misaltata a matsayin wacce ta bada mamaki matuka wajen zage damtse da yin aiki tukuru wajen zama a wannan tarihin na duniya baki daya, sun ce, ta yi aiki sosai ta kuma jure.
Daya daga cikin ahlinta, Chisom Nwafor, ta shaida wa LEADERSHIP cewa, ‘yar uwan tasu tana da hali mai kyau, tana faran-faran da kowa, kuma mai son nasara da sanya abun da ta sa a gaba da naci da dagewa.
Chisholm wacce ita ma take dafa abinci a Calabar Pot, kuma tana safaran abinci ma ta yanar gizo, ta ce, Hilda ta fara dafa abinci tsawon shekaru kuma tana matukar sha’awar abun da take yi, “Na yi matukar farin ciki domin ta cimma nasara kan mafarkinta na tsawon lokaci. Ta jima da wannan burin nata,” ta shaida.
- Tabbas Allah Mai Iko Ne Kan Komai, A Cewar Mahaifiyar Hilda
A bangaren mahaifiyar Hilda kuwa, Misis Lynda Ndukwe, cike take da murna da cigaba da godiya da jinjina ga Allah. Ta ce, ba za ta daina godiya ga Allah ba da ya dafa mata a kowani lokaci.
Ta ce, diyarta ta kasance wacce ta canza musu tarihi ta hanyar kafa tarihin da za su jima suna alfahari da ita, ta ce mafarki ne ya zama gaskiya domin diyar nata ta cimma da wannan burin a cikin ranta.
Sai ta gode wa fitaccen malamin nan, Fasto Jerry Eze, wacce ta ce ita kanta diyar nata ma za ta kasance mai mai yi masa yabo.
Ndukwe wacce ita ce shugaban wurin dafa abinci na Calabar Pot ta kasance jigon taimaka wa diyarta tun lokacin da ta fara buga-bugar shiga gasar har zuwa lokacin da ta yi nasara. An yi ta ganota a yanar gizo tana godiya wa Allah.
Shugaba Buhari, Osinbajo, Gwamnoni da wasu fitattun mutane sun taya Sarauniyar Girki, Hilda Barci Murna
Har-ila-yau, shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya taya sarauniyar dafa abinci, Hilda Bassey Effiong murnar lashe gasar dafa abinci mafi tsawo na Guinness, da cewa ta daukaka kimar Nijeriya.
Buhari a sanarwar da kakakinsa Femi Adesina ya fitar, ya yaba da kwazo, himma, azama da sa’ayin Hilda, yana mai cewa hakan wani mataki ne da zai kara kyautata tattalin arziki.
Buhari ya ce, Hilda wacce ta kasance mai gudanar da wurin sayar da abinci a Legas, ta koyar da wasu sosai kan yadda za su tsayu da kafafunsu yanzu kuma ta samu tagomashi a duniya baki daya.
Buhari ya nuna kwarin guiwarsa na cewa yadda Hilda ta dage wajen cimma burinta, hakan zai farkar da ‘yan Nijeriya da dama su ma su dumfari mafarkinsu ta yadda za su ga sun cimma nasara domin rayuwarsu take ingantuwa.
Kazalika, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, gwamnan Legas, zababben shugaban kasa Asiwajo Bola Ahmed Tinubu da sauran fitattun mutanen Nijeriya sun nuna farin cikinsu da taya Hilda murna tare da mata fatan cewa matasa da dama za su moreta.