A wani sakon faifan bidiyo wanda wakilin ‘yan uwa na harkar musulunci a Najeriya na yankin Sokoto Mal. Munir Mai Nasara ya fitar ya bayyana wanzuwar wasu bara gurbi masu zagayawa suna karbar kudade a hannun ‘yan siyasa da sunan zasu kawo musu kuri’un almajiran Sheikh Zakzaky.
Malam Munir ya bayyana hakan matsayin abinda ya sabawa ka’ida kuma hakan da sukayi bai dace ba domin babu wanda ya aike su kuma ba da sunan almajiran Sheikh Zakzaky din sukaje ba illah sunje ne a kashin kan su.
Malamin ya bayyana babban abin takaici a wannan lamari shine yadda wadannan mutane da sukaje wajen tsohon gwamnan Zamfara Abdul-azeez yari suka bayyana wai Sheikh Zakzaky ne ya turo su, alhali ba shine ya turo su ba.
Ya kuma bayyana cewa tuni Sheikh Zakzaky yayi bayani dangane da wannan lamarin saboda haka duk wanda yaje yayi irin wannan aiki a sani yayi ne a kashin kan sa.
A karshe Malam Munir ya bayyana cewa, babban sakon da yake so ya isar ga masoya dama mambobin harkar ta musulunci a Najeriya shine: Ba Hannun harkar Islamiyya abinda ya shafi siyasa musamman ma wanda suka zo suka gana da tsohon gwamnan jihar Zamfara, gaskiyar magana sunyi gaban kan su ne ba Jagora ya umarce su ba kuma ba da yawun harka sukayi ba” kamar yadda Malam Munir ya bayyana.
Ko a watannin baya ma lokacin da kwamitin siyasa na harkar musuluncin a Najeriya suka kaiwa Jagoran ta Sheikh Ibrahim Yaqoob Al-zakzaky ziyara a gidan sa dake Abuja ya bayyana damuwar sa kan yadda wasu bara gurbi ke amfani da sunan sa suka karbar kudi a hannun ‘yan siyasa da sunan zasu kawo musu kuri’un almajiran sa.
Inda yayi kira ga ‘yan siyasa da su kiyaye kada su fada hannun irin wadannan marasa gaskiya masu kokarin bata sunan bayin Allah saboda son zuciya.