Akalla mutane uku ne aka tabbatar da mutuwarsu tare da jikkata wasu da dama bayan wani harbe-harbe a birnin New Mexico na kasar Amurka.
Ofishin Sheriff na gundumar San Juan ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.
‘Yansanda sun ce an kashe wadanda abun ya shafa, inda suka ce ciki har da jami’ai biyu.
Harbin ya faru ne da safiyar Litinin a kusa da wani wurin shakatawa na jama’a.
“A wannan lokacin, bayanan da muke samu sun bayyana cewa jami’an ‘yansanda da yawa na Farmington harin ya rutsa da su. An yi arangama da mutum daya da ake zargin dan bindiga ne tare da kashe shi a wurin,” in ji sanarwar.
“Ba a san asalin wanda ake zargin ba kuma babu wata barazanar da aka sani a yanzu.
“An harbi jami’ai biyu, daya daga Sashen ‘yansanda na Farmington daya kuma daga ‘yansandan Jihar New Mexico, wadanda a halin yanzu suke a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Yanki ta San Juan inda suke jinyar raunukan da suka samu.
“Akwai fararen hula da dama da abin ya shafa wanda akalla mutum uku suka mutu.
‘Yansandan sun bukaci mazauna yankin da su guji yankin da kuma zabar wasu hanyoyin tafiya.
An sanya dokar hana fita a yankin, wanda ke nufin cewa ayyukan makaranta suna tafiya kamar yadda aka saba, amma ba a bar kowa ya fito a waje ba, kuma iyaye za su iya daukar dalibai, in ji Roberto Taboada, kakakin Makarantun Municipal Farmington.