Har yanzu Ba’a san Makomar Fasinjoji 168 Ba Bayan Mako Daya Da Kai Harin Jirgin Kasa A Najeriya.
Hukumar kula da ziraga zirgr jiragen kasa ta najeriya ta bayyana cewa takardar dake hanunta ta nuna cewa akwai pasinjoji 362 a cikin jirgin kafin yan bindigan su kai masa Hari, da yayi sanadiyar kashe mutane 8 tare da jikkata wasu da dama, yayin da wani adadi da ba’asani ba yayi batan dabo.
Ana sa bangaren Manajan Daraktan kamfanin Fidet Okhiria ya an sake gano mutane 14 da suka kubuta bayan harin da hakan ya cika adadin mutane da suka tsira bayan harin su 186, yazuwa yanzu dai ba’a da cikakkaiyar masaniya ko mutane 168 da ba’a gani ba bayan harin an yi garkuwa das u ne ko ko A’a.
A makon day a gabata ne wasu yan ta’adda dauke da makama suka kai harin kan jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna dake Arwa masu yammacin Najeriya inda suka tarwasta layin dogon kafin daga bisani suka buke wuta kan mai uwa da wabi a cikin jirgin.
READ MORE : Iran Tace Har yanzu Bata Ga Martanin Amurka Kan Tattaunawar Vieana Ba.
Tuni dai yan ta’adan suka kira iyalan wasu daga cikin pasinjojin da suek tsare da su, yace: “ lambobin wayar mutane 146 da aka kira ko dai suna kashe, ko kuma suna ta kara ba’a dauka ba, tun washe garin kai harin da safe.