Shugaban kungiyar magoya bayan Matawalle a jihar Sokoto kuama na hannun daman sa da daruruwan magoya bayansa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC Jagoran masu sauya shekar, Alhaji Anas Waziri, ya bayyana cewa akwai karin ‘ya’yan PDP da za su biyo su zuwa jam’iyyar mai mulki a kasar.
Shugaban kungiyar magoya bayan Matawalle a jihar Sokoto, Alhaji Anas Waziri, da daruruwan masu mara masa baya sun sauya sheka daga People’s Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Bashar Abubakar, babban mai ba Sanata Aliyu Wamakko shawara a shafukan sada zumunta na zamani, a ranar Lahadi a Sokoto, PM News ta rahoto.
Abubakar ya nakalto Waziri yana cewa: “Mun yanke shawarar barin jam’iyyar saboda shugabanninta sun gaza kaimu inda muke mafarkin zuwa.
“Barinmu PDP alamun nasara ne ga APC saboda karbuwar da ta samu a koina.” Waziri ya bayyana cewa akwai karin mambobin PDP da za su biyo sahunsu zuwa APC.
Ya bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Alhaji Ahmad Aliyu a matsayin wanda yafi dacewa da mutanen jihar domin yana samun karin magoya baya.
Da ya tarbi masu sauya shekar, Aliyu ya fada masu cewa za a dama dasu kamar kowa a jam’iyyar.
Ya kuma dauki alkawarin tafiya da kowa a gwamnati idan har aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar, rahoton Daily Post.
A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu mambobin jam’iyyar siyasa a jihar Oyo sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin babban zaben 2023.
Masu sauya shekar sun samu tarba a ranar Asabar yayin wani taron jam’iyyar da ya gudana a makarantar sakandare na Elekuro, Ogbere a yankin Ona-Ara da ke jihar.
Wadanda suka jagoranci taron na maraba da zuwa sune, Sanata Teslim Folarin, dan takarar gwamna na APC a jihar da Dr Yunus Akintunde, dan takarar sanata mai wakiltan Oyo ta tsakiya, PM News ta rahoto.
Source:legithausang