TRT ta rawaito cewa, hambararriyar gwamnatin Nijar ta nemi Faransa ta dauki matakin soji domin kubutar da Mohamed Bazoum a awannin farko bayan juyin mulkin soji na ranar 26 ga watan Yuli, kamar yadda aka tabbatar ranar Asabar.
“Lokacin da muka tabbatar cewa juyin mulki aka yi a awannin farko, Firaiministan rikon kwarya Massaoudou ya nemi agajin Faransa, wanda ba sabon abu ba ne,” a cewar daya daga cikin masu bai wa Bazoum shawara, wanda ya nemi a boye sunansa, a hirarsa da jaridar Le Monde.
A cewar jaridar ta Faransa, an yi nazari sosai game da yiwuwar aiwatar da wannan bukata.
Gwamnatin Bazoum ta yi kawance da kasashen Yammacin duniya a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya da kuma hana ‘yan ci-rani bi ta Bahar Rum domin isa Turai.
Faransa, wacce ta yi wa Nijar mulkin-mallaka har zuwa shekarar 1960, tana da sojoji 1,500 a kasar, wadanda suke aikin hadin gwiwa da dakarun gwamnati.
A baya gwamnatin sojin, wadda ke karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani, kwamandan sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar, ta yi zargin cewa hambararriyar gwamnatin ta bayar da umarni ga Faransa ta kaddamar da hari a fadar domin kubutar da Bazoum.
Source: LeadershipHausa