Hafsan hafsoshin sojin kasa, Janar Taoreed Lagbaja ya mika sakon neman afuwa daga al’ummar Jihar Kaduna, sakamakon harin bam din da sojoji suka kai wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan sama da mutane 85.
Yayin da yake jawabi cikin alhini lokacin da ya kai ziyara kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi, Janar Lagbaja ya bayyana bakin cikinsa da lamarin.
Kakakin rundunar Janar Onyema Nwachukwu, ya ce hafsan hafsoshin ya bayyana cewar a ‘yan makonnin da suka gabata, ‘yan ta’adda sun kutsa kai a wannan yankin, abin da ya sa sojoji suka kaddamar da hare-hare, kuma sakamakon haka ne na’urarsu ta gano taron dandazon mutane a wurin Maulidin da aka kai musu hari cikin kuskure.
Lagbaja ya ce abin da ya sa ya ziyarci kauyen da kansa shi ne ya jajanta wa al’ummar yankin kan faruwar lamarin.
Hafsan ya ce ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano inda aka samu kuskure, domin taimaka musu wajen inganta ayyukansu nan gaba.
A nasa jawabi, Hakimin Rigasa, Aminu Idris ya ce duk da zafin kisan da suke ji, sun gamsu da yadda rundunar sojin ta nuna damuwa da kuma amsa kuskuren da jami’anta suka yi dangane da kai harin, yayin da ya bukaci kai dauki ga iyalan wadanda abun ya shafa.
Hakimin, ya yi karin hasken cewar cikin wadanda harin ya rutsa da su har da Kiristocin da ke zaune a garin.
Daga bisani Janar Lagbaja ya jagoranci tawagarsa zuwa asibitin Barau Dikko domin duba wadanda suka jikkata.
Tuni kungiyoyi da daidaikun mutane suka shiga nuna alhininsu kan harin bam din da ya yi sanadin mutuwar masu taron Mauludin.
Sai dai lamarin ya dauki zafi a kafafen sada zumunta, inda mutane ke ganin wannan lamari a matsayin babban kuskure kuma dole ne a dauki mataki.
Source: LEADERSHIPHAUSA