Hadimin gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi murabus daga kan mukaminsa kan wasu dalilai na kashin kansa.
Ibrahim Attahiru, mashawarci na musamman kan harkokin wasanni da matasa ya gode wa gwamnan bisa damar da ya ba shi.
Jam’iyyar APC mai mulki na fama da rigingimun cikin gida a jihar Kwara yayin da gwamnan ke kokarin yin tazarce.
Ibrahim Attahiru, mai baiwa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, shawara kan harkokin wasanni da ci gaban matasa ya yi murabus.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hadimin gwamnan ya bayyana matakin da ya ɗauka ne ranar Lahadi a wata wasiƙa da ya aike wa mai girma gwamna, inda yace ya yi haka saboda wasu dalilai na ƙashin kansa.
A wani bangaren Wasikar da PM News ta ruwaito, Attahiru ya ce: “Mai girma gwamnan ina son ka sani cewa na yi murabus ne saboda wasu dalilai na ƙashin kaina.”
“Ina miƙa godiya ta ga mai girma zaɓaɓɓen gwamnann jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, bisa wannan dama da aka bani kuma da yarda da ni.”
Wannan murabus din na mashawarcin gwamnan na musamman ya zo ne a lokacin da rigingimu suka hana jam’iyyar APC mai mulkin jihar Kwara zaman lafiya.
A kwanakin baya ɗaya daga cikin jagororin da suka hana idonsu bacci a tafiyar O’to Ge da ta kai APC ga nasara a 2019 ya aje aikinsa a gwamnatin jihar Kwara.
Lamarin dai ya samo asali ke daga wata ziyara da aka hangi jigon PDP kuma tsohon shugaban majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya kai masa har Ofis a Ilorin.
Jam’iyyar APC na fama da rikici iri daban-daban yayin da gwamnan ke yunkurin ganin ya yi tazarce a kujerarsa a babban zaɓen 2023.
Mambobin Jam’iyyar APC da LP Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A wani labarin kuma jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Taraba, arewa maso gabashin Najeriya ta samu karin magoya baya a karshen makon nna.
Wasu bayanai sun nuna cewa dubbannin mambobi daga jam’iyyun adawa, APC, LP da sauransu, sun koma tsagin PDP a shiyyar Sanatan kudancin Taraba.
Masana harkokin siyasa a jihar sun yi hasashen cewa za’a iya samun karin masu sauya sheƙa nan gaba idan yaƙin neman zaɓe ya kankama.
Source:LEGITHAUSA