A ranar Alhamis mai zuwa Shugaban Kasa, Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Ngelale, ya ce, Tinubu zai halarci zaman taron shugabannin kasashe da gwamnatocin Tarayyar Afirka (AU) karo na 37.
Taken taron na bana shi ne ”Koyar da kasashen Afirka dabarun da suka dace a karni na 21: Gina tsarin ilimi mai nagarta don kara samun dama ga ci gaban ilimi, tsawon rai, inganci, da kuma dacewa da koyo a Afirka”.
Ngelale ya ce, shugaban zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka a manyan tarukan da suka shafi sauye-sauyen hukumomin kungiyar ta AU, da zaman lafiya da tsaro, musamman batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, da kuma hanyoyin shiga da kuma abubuwan da suka sa a gaba a kungiyar ta G20.
Kazalika, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, Tinubu zai kuma halarci wani babban taro na musamman na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS a matsayinsa na shugaban kungiyar a yankin.
Ya ce shugaban wanda zai samu rakiyar ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati a wannan tafiya ana sa ran zai dawo Abuja a bayan kammala taron a habasha.
Ngelale ya ce, shugaban zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka a manyan tarukan da suka shafi sauye-sauyen hukumomin kungiyar ta AU, da zaman lafiya da tsaro, musamman batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, da kuma hanyoyin shiga da kuma abubuwan da suka sa a gaba a kungiyar ta G20.
Kazalika, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, Tinubu zai kuma halarci wani babban taro na musamman na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS a matsayinsa na shugaban kungiyar a yankin.
Ya ce shugaban wanda zai samu rakiyar ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati a wannan tafiya ana sa ran zai dawo Abuja a bayan kammala taron.
Source: LEADERSHIPHAUSA