Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, gwamnonin yankin kudancin Najeriya sun shiga wata ganawar sirri.
Ana kyautata zaton za su tattauna ne kam lamurran da suka shafi tsaro da lamuran yankinsu da zaman lafiya.
Hakazalika, an ce za su tattauna kan lamarin da za ya shafi ci gaba da tsare Nnamdi Kanu, shugaban ‘yan IPOB.
Gwamnonin Ebonyi, Enugu da Abia da mataimakin gwamnan Anambra da Imo sun shiga wata ganawar sirri a gidan gwamnatin jihar Enugu, Vanguard ta ruwaito.
Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi wanda kuma shine shugaban gwamnonin Kudu maso Gabas ne ke jagorantar zaman na gwamnoni da mataimakansu.
Ana kyautata zaton cewa, daya daga abin da za a tattauna a zaman ya hada batun shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Hakazalika, an ce za su tattauna kan lamarin da ya shafi tsaron yankin, tare da nemo mafita ga matsalolin tsaro.
Idan baku manta ba, a kwanakin da suka gabata ne aka sace wasu mutane 30 kusa da titin Enugu zuwa Nsukka, ciki har da hadimin gwamna da dalibai.
A bangaren Nnamdi Kanu, an tsare shi tare da gurfanar dashi a gaban kotu tun shekarar da ta gabata.
Kotu ta ba da umarnin a sake shi, amma hukumomin gwamnati na ci gaba da bincike kan lamarinsa tare da bayyana dage kara.
Wadanda suka halarci zaman Daga cikin wadanda suka halarci zaman sun hada da gwamna Rt. Hon. Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, Okezie Ikpeazu na jihar Abia da David Umahi na jihar Ebonyi, rahoton Daily Post.
Hakazalika da Prof. Charles Soludo na jihar Anambra da Hope Uzodinma na jihar Imo.
Wadannan gwamnoni biyu sun samu wakilcin mataimakansu ne; Dr. Onyekachukwu Ibezi da Prof. Placid Njoku.
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankala, amma su kasance a ankare kan shawarwarin tsaro da kasashen turai suka fara bayarwa kan birnin tarayya Abuja.
A cewar wata sanarwa da Buhari ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya shawarci ‘yan kasa da jami’an tsaro da su zama masu sanya ido kan lamarin tsaron kasar nan.
Idan baku manta ba, a makon nan ne kasar Amurka ta ba ‘ya’yanta shawarin fara barin Najeriya sakamakon tsoron barazanar tsaro da ka iya biyo baya a babban birnin tarayya Abuja.
Source:legithausang