Wasu gwamnoni a Najeriya na duba yiwuwar fara ba ‘yan banga bindigogi AK-47 domin dakile rashin tsaro.
Gwamnatin Najeriya ta sha bayyanawa karara cewa, ba daidai bane jihohi su mallaki makamai masu sarrafa kan su.
Ana yawan samun hare-hare da tashe-tashen hankula a Najeriya, lamarin dake sanya nemo mafita ga rashin tsaro.
Lucky Irabor, shugaban hafson tsaro a Najeriya ya ce babu jihar da gwamnati ta ba ikon mallakar makamai masu sarrafa kansu musamman ga ‘yan banga.
Ya bayana hakan ne a wata hira a ranar Juma’a da manema labarai bayan wani taron majalisar tsaro na kasa da aka gudanar a Abuja.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman da aka yi, inji rahoton jaridar TheCable.
Da yake kaddamar da zubin farko na jami’an tsaron da jiharsa ta samar a watan Agusta, gwamna Ortom ya ce zai samar da makamai masu sarrafa kansu ga wadannan ‘yan bangan.
Gwamnoni na yunkurin ba ‘yan banga bindiga AK-47 A nasa bangare, gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a watan Satumba ya ce, zai yi kokarin samarwa ‘yan bangan Amotekun dake jiharsa bindiga.
Da yake martani ga wadannan maganganu, Irabor ya ce, gwamnatin tarayya ne ke da alhakin ba da izinin amfani da bindiga, misali AK-47.
A cewarsa: “Makamai sun kasu ne gida biyu. Kuna da makamai masu sarrafa kansu da kuma wadanda ba masu sarrafa kansu ba, wadanda wasun ku na da shi idan kuka nemi lasisin mallakarsu.”
Daga nan ya bayyana cewa, idan dai makami mai sarrafa kansa, to tabbas babu jihar da gwamnati ta ba damar mallaka.
Daga karshe ya shaidawa jihohi cewa: “Don haka, ba za ku tambayi abin da baku da ikon mallaka ba.”
Source: legithausang