Yayin da sauran kasashen duniya suka yi nisa da kwashe ‘yan kasashensu daga Sudan mai fama da tashin hankali, Nijeriya ta ce yau ko gobe za ta fara jigiliar ‘yan Gwamnatin Nijeriya mazauna Sudan wadanda suka fara kokawa da irin tsaka mai wuyar da suke ciki.
Ministan Harkokin wajen Nijeriya Mists Jeoferry Onyeama ya ba da tabbacin cewa daga yau zuwa gobe za a fara kwaso ‘yan Nijeriya daga Sudan, inda rikicin cikin gida ke ci gaba da kara tsananta.
Ministan, ya ce suna jiran sahalewar gwamnatin Sudan ne da nufin fara kai ‘yan Nijeriya zuwa makwabciya, kasar Masar, daga inda za a yi jigilar su domin dawo da su gida Nijariya.
Ya kuma kara da cewa, tuni aka fara tattaunawa da ofisoshin jakadancin Nijeirya da ke Masar da Sudan domin tsara yadda za a yi jigilar.
A daidai lokacin da Amurka ta yi amfani da jiragen yaki domin kwashe jami’an diflomassiyarta, sama da dari daga birnin Khartoum su ma kasashe irin su Faransa, Jamus da dai sauran kasashe, tuni suka yi nisa wurin kwashe mutanensu da ke Sudan.