Gwamnatin Najeriya Ta Tabbatarwa Da “Yan Kasar Mazauna Ukiraniya Cewa Za A Fitar Da Su.
Ministan harkokin wajen Najeriya Geofery Onyeama ne ya bai wa ‘yan Nigeria mazauna Ukiraniya tabbacin cewa za a dauke su daga kasar.
Onyeama wanda ya gabatar da taron manema labaru a birnin Abuja ya ce; Gwamnatin tarayyar Najeriya tana kokarin aikewa da jirgi na musamman zuwa kasar ta Ukiraniya domin fito da ‘yan kasar daga ciki.
Har ila yau ministan harkokin wajen na Najeriya ya cigaba da cewa; An tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake birnin Kiev inda aka sanar da shi su shirya dauko ‘yan kasar da suke da sha’awar komawa gida,musamman mazauna yankunan Donestk da Luthensk.
Da akwai daliban Nigeria da kuma ‘yan wasan kwallon kafa masu yawa da suke a kasar ta Ukiraniya, kuma tun barkewar yakin ne suke yin kira ga mahukuntan kasarsu domin fitar da su waje.