Ministan kula da al’amuran yan sanda a Najeriya Maigari Dingyadi ya shaidawa manema labarai cewa Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da sabon tsarin biyan jami’an yan sanda kudaden alawus – alawus da kaso 20 cikin 100, kuma zai fara aiki daga farkon watan Janerun shekara ta 2022.
Yace batun Karin Albashin yan sanda yana daga cikin kokarin da gwamnatin buhari take yi na bukatun da aka gabatar mata a lokacin Alkawarin zanga zangar End Sars da aka yi a birnin Ikko,
Daga cikin Bukatu guda 5 da masu zanga-zangar suka gabatarwar wajen gwamnati sun hada da biyan diya ga iyalan wadanda abin ya shafa a lokacin tarzomar , da kuma kara albashin jami’an yan sanda.
Daga karshe taron na majalisar zartarwa ta kasa da shugaba buhari ya jagoranta a fadar Aso a jiya laraba ya amince da Karin alawsu –alawus din yan sanda na fita sintiri da kasha 6, kana an ware kudi har Naira miliyan niliyan a.2 domin biyan kudaden inshore da sauran wasu hakkokin.