Gwamnatin mulkin sojin Nijar na neman ɗauki daga Rasha
Dakarun sojin Nijar da suka yi wa gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum juyin mulki na kira ga ƙasar Rasha da ta kawo musu dauki, tare da neman ƙasar Faransa da sauran ƙasashen yamma da ke ƙasar da su fice da Nijar ɗin.
Cikin wata sanarwa ta kakakin majalisar ceto ƙasar ta sojoji Kanal Manjo Amadu Abdurahamane, ya karanta a gidan talbijin na ƙasar ya yi kira ga ƙasar Rasha da ta taimaka wa Nijar da sojoji da kayan aiki.
A yau ne ƙungiyar Ecowas ke gudanar da taro don tattauna batun juyin mulkin da sojojin suka yi a Nijar.
To sai dai cikin sanarwar da majalisar ceton ta Nijar ta fitar, ta yi zargin cewa taron na Ecowas yunƙuri ne far wa Nijar da yaƙi.
A don haka ne ma Kanal Manjo Amadu Abdurahamane ya ce a shirye suke su kare ƙasarsu daga hare-haren da ya yi zargin Ecowas za ta ƙaddamar wa ƙasar.
Sannan kuma ya yi kira ga ‘yan ƙasar da su fito su gudanar da zanga-zanga domin mara musu baya.
Ƙasar Rasha dai na da dakaru a Mali mai makwabtaka ta Nijar, lamarin da ya sa Faransa da Majalisar Dinkin Duniya suka janye sojojinsu da ke aikin wanzar da zaman lafiya daga ƙasar.
A ranar Laraba ne dai sojojin Nijar suka sanar da kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum, lamarin da ya sa ƙasashen duniya da ƙungiyoyi ke ci gaba da yin Allah wadai da abin da sojojin suka yi, tare da kira da su maido da mulkin fara hula da kuma sakin shugaban ƙasar wanda suke tare da shi.
Ko a ranar Asabar ma ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU ta bai wa sojojin ƙasar wa’adin kwanaki 15 da su koma barikokinsu tare da maido da mulkin fara hula a ƙasar.