Gwamnatin Jihar Katsina ta jaddada kudurinta na samar da gine-gine tare da gyara wadanda take da su a yankunan karkara a karkashin shirin nan na samar da kayayyakin more rayuwa da farfado da tattalin arzikin yankunan karkara.
Kwamishinan kula da cigaban yankunan karkara, Injiniya Mustapha Mahmud Kanti Bello ya sanar hakan a lokacin da yake kaddamar da aikin gyaran cibiyar kiwon lafiya ta Yandi da ke karamar hukumar Mai’adua.
Kamar yadda ya ce shirin gwamnatin na samar da kayayyakin more rayuwa da farfado da tattalin arzikin yankunan karkara yana da bangarori da dama da suka hada da ginawa da kuma gyara cibiyoyin kiwon lafiya da gina rijiyoyin burtsatse da sauransu.
Injiniya Kanti Bello ya yi nuni da cewa a karkashin shirin gyara cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnatin za a gyara cibiyoyin kiwon lafiya guda takwas a kananan hukumomi takwas da ke jihar.
Ya bayyana cewa tuni a kashi na farko na shirin an gina rijiyoyin burtsatse 70, sannan kuma an tallafa wa matasa 60 wajen horar da su harkokin kasuwanci.
Ya kara da cewa ana gudanar da shirye-shirye na samar da jari ga matasan da aka horar domin su fara kasuwancinsu wajen dogaro da kai.
Mukaddashin babban sakatare na ma’aikatar, Alhaji Tanimu Bagiwa ya ce shirin na samar da kayayyakin more rayuwa da kuma bunkasa tattalin arzikin yankunan karkara na da nufin sake gyara gine-gine da kuma tallafa wa matasa da mata a yankunan karkara.