Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayyana kudurin sake gina katafaren shatale-talen gidan gwamnatin jihar da aka rusa a kwanakin baya a wani wuri mafi da cewa – gadar Naibawa da ke wajen birnin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin da yake gana wa da mai zanen shatale-talen ‘Golden Jubilee’ Kaltume Gana a sabon wurin da za a sake gina shatale-talen.
Gwamnan Yusuf ya sake nanata kudirin gwamnatisa na samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar.
Ya ce wurin ya dace da zanen kuma ba zai haifar da wani kalubalen tsaro ba bayan gudanar da cikakken bincike, ya kuma sake tabbatar wa ‘yan jihar cigaba da samar da ayyukan more rayuwa masu inganci.
Mai zanen, Kaltume Gana ta gode wa gwamnan bisa yaba wa da aikinta na kwarewa da fasaha ta musamman.
A wani labarin na daban gwamnatin jihar Katsina ta bayar da hutun mako guda ga daliban makarantun Firamare da Sakandare domin gudanar da bukukuwan sallar idin layya a jihar.
Sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mukaddashin babban sakataren ma’aikatar ilimi, Ya’u Jibrin, wadda jaridar LEADERSHIP ta samu kwafinta a ranar Lahadi.
“An ba da wannan hutun ne na mako guda ga daukacin Makarantun Gwamnati da masu zaman kansu a fadin Jihar daga ranar Litinin 26 ga watan Yuni zuwa Litinin 3 ga Yuli, 2023,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran daliban makarantar kwana za su koma makarantun su a ranar Lahadi 2 ga Yuli, 2023.
Sabida haka, ma’aikatar ilimi ta na yi wa daukacin ma’aikata da dalibai barka da Sallah.