Gwamnatin Kano ta ɗage ziyarar da Buhari zai kai domin buɗe manyan ayyuka
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun aika wa fadar shugaban ƙasar Najeriya cewa, sun ɗage ziyarar da aka tsara Shugaba Muhammadu Buhari zai yi a Jihar domin buɗe wasu manyan ayyukan raya ƙasa.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnan Abba Anwar ya fitar ranar Asabar, ya ce Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wani taro da malamai da shugabannin siyasada sauran masu ruwa da tsaki a gidan gwamnati, ya ce an dauki matakin ne domin kaucewa faruwar abin da ba zai yi daɗi ba.
A cewar Gwamnatin, akwai buƙatar lura da halin da ake ciki na matsi saboda wa’adin daina amfani da tsofaffin kuɗi da CBN ya gindayawa mutanen Najeriya, akwai kuma matsalar tsaro, duka sai an yi nazari a kansu.
A ziyarar da Shugaba Buhari ya je Katsina ne aka samu wani rikici da ya ja aka riƙa jifan motoci da kuma ƙona tayoyi a kan titi, nuna fushi ga matsalolin da ake ciki na ƙarancin man fetur da kuma wa’adin tsofaffin kuɗaɗe.
Read More :
Atiku ya roƙi CBN ya ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗi.
Canjin Kuɗi: Gwamnatin Kano Ta Dage Ziyarar da Shugaba Buhari Zai Kawo Jihar.