Gwamnatin Kamaru za ta hukunta masu yaɗa jita-jitar juyin mulki
Ministan sadarwa na ƙasar Kamaru, Rene Emmanuel Sadi, ya yi gargadi game da raɗe-raɗin da ake yi cewa kasar na iya fuskantar juyin mulki, a daidai lokacin da ake fama da matsalar a ƙasashen Afirka waɗanda Faransa ta yi wa mulkin mallaka.
A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin kasar ya fitar, ya bayyana Kamaru a matsayin ƙasa ta masu bin doka tare da barazanar kamawa da hukunta masu hasashen juyin mulki a ƙasar.
“Saboda haka gwamnati ta buƙaci mutane da su yi taka-tsan-tsan don kada su yaɗa jita-jitar juyin mulki da kuma hasashen makomar Kamaru, lamarin da zai iya tayar da zaune tsaye a ƙasar” in ji shi.
Tun bayan da sojoji a Gabon suka kwace mulki daga hannun Ali Bongo a ranar 30 ga watan Agusta, masu sharhi kan shafukan sada zumunta ke ci gaba da ƙara nuna yiwuwar juyin mulki a makwabciyarta, kasar Kamaru.
Shugaba Paul Biya mai shekaru 90 wanda ya tsallake rijiya da baya a yunƙurin juyin mulki a ƙasar a shekarar 1984 ya shafe shekaru 41 yana mulkin Kamaru.
Magoya bayansa na neman ya sake tsayawa takara a zaben 2025.
Read More :
Jamus ta soki yadda Netanyahu ya nuna taswirar karya a zauren Majalisar.