Tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, musulmin birnin Edmonton na kasar Canada sun yi lale marhabin da matakin hukunci na doka a kan masu cutar da mutane saboda dalilai na addini wanda gwamnatin jihar ta fitar.
Rahoton ya ce, tun kafin wannan lokacin majalisar dokokin jihar ta taba kafa irin wannan doka amma daga bisani aka jingine yin aiki da ita.
A halin yanzu wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin sun sake gabatar da wani kudiri da ke neman a sake dawo da yin aiki da wannan doka.
Yanzu haka an sanya ranar Litinin mai zuwa ta zama tattauna wanann kudiri, da kuma yanke matsaya guda a kansa, inda ake sa ran galibin ‘yan majalisar za su amince da hakan.
Daga cikin matakan da dokar za ta kunsa, duk wanda aka kama shi da laifin cin zarafin wani saboda banbancin addini ko launin fata ko kabila, to zai fuskanci hukunci bisa wanann doka, sannan kuma za a yi masa tara wadda zata fara daga dala dari biyu da hamsin, idan ya kara za a rubanya tarar a kansa.
Musulmin kasar Canada sun yi lale marhabin da wannan mataki na gwamnatin tare da yin kira ga ‘yan majalisar da su amince a aiwatar da wannan kudiri kamar yadda aka tsara shi.
Musulmi dai a kasashe da dama musamman a kasashen yammacin turai, sai dai an tabbatar da cewar musulmi sun fi fuskantar takurawa a kasashen da wahabiyanci yayi tasiri, musamman hakan yafi shafar mabiya darikun sufaye da kuma mabiya mazhabar shi’anci.
Kasashe irin su saudiyya wadanda tuntuni suka daurewa akidar wahabiyanci baya basu yadda da kowacce irin akida sai ta wahabiyancin wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa na kare hakkin dan adam.
Ana sa ran mabiya addinai a fadin duniya su samu sassauci idan aka samar da dokoki da zasu bama kowa damar gudanar da addini ba tare da tsangwama ba.