Bayanai sun fara fitowa game da alkawuran da gwamnati ta yiwa kungiyar malaman jami’a ASUU.
Ana kyautata zaton dai ASUU zata janye daga yajin aikin biyo bayan shiga tsakani da Kakakin majalisa yayi.
Kawo yanzu akwai wata Jerin Jami’o’in Najeriya 22 Da Suka Zabi A Dakatar Da Yajin Aikin.
Punch ta ruwaito cewa za’a mayar da ragamar biyan kudin alawus na ma’aikatan jami’o’in Najeriya hannun majalisar jagorancin jami’o’in gwamnatin tarayya daga 2024.
Hakazalika gwamnati za ta saki kudi naira bilyan hamsin (N50bn) don biyan kudin bashi na alawus da Malaman ke bi kafin lokacin.
Wata majiya cikin majalisar zartaswar ASUU ta bayyana hakan ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.
A cewar majiyar: “Game da lamarin alawus, an tanadi Bilyan 50 don biyan bashin da muke bi yayinda aka tanadi N170bn na karin albashi.”
“Amma daga 2024, majalisar jagorancin jami’o’i ne zasu rika biyan alawus yayinda za’a zuba N300 billion wajen gyara makarantu.”
Mambobin ASUU sun fara zama Zaku tuna cewa mun bayyana muku rassan ASUU a fadin tarayya sun fara tattaunawa bisa tayin da gwamnati tayi musu.
A yau ake sa ran majalisar zartaswar kungiyar za ta zauna don yanke shawara.
Biyo bayan umurnin da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i na kasa, ASUU, sassa da dama na malaman jami’an yanzu sun zabi a dakatar da yajin aikin da suka shafe watanni ana yi.
Deborah Tolu-Kolawale, yar jarida mai aiki da The Punch, ce ta bayyana hakan a rubutun da ta yi a Twitter.
A cewar yar jaridar na makarantun gaba da sakandare, ga jerin jami’o’in da suka zabi a janye yajin aikin bisa sharadi ko umurnin kotu.
Source:legithausang