Gwamnati a jihar Kano mai jiran gado karkashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf ta bayyana aniyarta na kwato kadarorin al’umma da ake zargin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sayar wa ‘yan’uwansa.
A cewar Dr. Abdullahi Baffa Bichi, shugaban kwamitin amso kadarorin gwamnati na jam’iyyar NNPP mai shirin karbar mulki, tace an sayar da ofishin hukumar da ke kula da bin doka da ke kan titin State Road a kan kudi kalilan – naira miliyan 10 ga Abba Ganduje, amma yanzu an kimanta kudin ginin akan kudi sama da Naira miliyan 300.
A wata sanarwa da Dr. Bichi ya raba wa manema labarai a Kano, ya nuna matukar damuwarsa game da abin da gwnatin mai barin gado ta yi, wanda ya bayyana a matsayin barnatar da dukiyoyin jama’a.
Ya kara da cewa gwamnati mai jiran gado za ta nemo duk wata hanya ta doka da ta dace don kwato kadarorin jama’a da ake zargin an sayar da su.
A wani labarin na daban zaunannen mataimakin wakilin kasar Sin dake MDD Dai Bing ya yi tsokaci yayin taron da kwamitin sulhun majalisar ya kira domin tattauna kan yanayin da yankin Abyei ke ciki jiya Talata 9 ga wannan wata da cewa, kasar Sin tana fatan rikicin kasar Sudan ba zai jawo mummunan tasiri kan batun yankin, kuma tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su ci gaba da yin kokari domin tabbatar da matsayin yankin Abyei yadda ya kamata.
Dai Bing ya kara da cewa, a makonnin baya bayan nan, shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta kudu sun taba bayyana cewa za su yi kokari domin daidaita batun game da matsayin yankin Abyei, amma abun bakin ciki shi ne Sudan ta shiga yanayin tangarda yanzu, don kasar Sin tana fatan Sudan za ta tsagaita bude wuta a kan lokaci, kuma ta hakake cewa, Sudan da Sudan ta kudu za su ci gaba da yin shawarwari da hadin gwiwa, ta yadda za su tabbatar da matsayar guda da suka cimma.
Kazalika, ya nuna cewa, kasar Sin ta yaba da kokarin da rundunar sojojin MDD dake yankin Abyei take yi domin tabbatar da tsaro a yankin, kuma za ta ci gaba da goyon bayan aikin rundunar sojojin ta hanyar daukar hakikanin matakai, ta yadda za ta taka rawar gani wajen kiyaye tsaro a yankin. (Mai fassarawa: Jamila)