Gwamnan Zamfara na zargin Gwamnatin Tarraya da ƙoƙarin sasanci da ƴan bindiga
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci gwamnatin tararraya ta gudanar da cikakken bincike game da wata tattaunawar sulhu ta sirri da ake yi da ƴan bindiga a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewar tawagar wasu hukumomi da Gwamnatin Tarayya ta aika sun fara tattaunawa da ƙungiyoyin ƴan bindiga ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.
A ranar Litinin Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar da wata sanarwa, ta nuna rashin jin dadin yadda wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya suka gana da ƴan bindiga ba tare da tuntuɓar gwamnati da hukumonin tsaron jihar ba.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewar: ”Gwamna Dauda Lawal ya buƙaci gwamnatin tarayya ta fayyace wannan mataki na wasu hukumominta, wanda ya ci karo da ƙudurin gwamnatin jihar na amfani da ƙarfi kan ƴan bindigar.
Ya ƙara da kira ga gwamnati ta binciki wannan lamari, wanda tamkar zagon ƙasa ne ga yunƙurin gwamnatin jihar na yaƙar ƴan fashin daji.
Gwamnatin Zamfara ta ce ta samu rahoton yadda jami`an gwamnatin tarayya suka gana da ƙungiyoyin ƴan fashin daji a yankunan Birnin Magaji da Maradun da Mun haye da Bawo da kuma Bagege.
“Yunƙurin yin sulhun da ƴan fashi da tsohuwar gamnatin jihar ta yi a baya bai yi tasiri ba. Ya kamata mu ɗauki darasi daga kura-kuran baya tare da ɗaukar sabbin hanyoyin dawo da zaman lafiya Zamfara.”
“Kasancewar yaƙi da fashin daji na cikin manyan ƙudurorin gwamnatin jihar Zamfara, ba za mu lamunci duk wani abu da zai kawo cikas ga hakan ba.”
Muna buƙatar Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mataki nan take ta hanyar dakatar da duk wata tattaunawa da ake yi da ƴan fashin daji a Zamafra, domin hakan zagon ƙasa ne ga matakan da ake ɗauka.” In ji sanarwar.