Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya jajanta wa takwaransa na jihar Filato, Gwamna Simon Bako Lalong da kuma mutanen jihar, kan rikicin baya -bayan nan da ya haddasa asarar rayuka da na dukiyoyi.
GwamnaGwamnan Sule, ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci tawagar manyan masu fada a ji daga Jihar Nasarawa tare da sashin shugabaninnin addinai Sule, ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci tawagar manyan masu fada a ji daga Jihar Nasarawa tare da sashin shugabaninnin addinai zuwa gidan gwamnatin da ke garin Jos.
Da yake nuna damuwarsa kan abin da ya faru a jihar Filato kwanan nan, Gwamnan Jihar Nasarawa ya ce ya kai ziyarar ne cikin yanayin ‘yan uwantaka da hadin kai ga Gwamna Lalong da jama’ar jihar musamman a irin wannan lokacin da jihar ta shiga halin damuwa. Gwamnan ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ke kokarin lalata zaman lafiya da aka samu a Jihar Filato.
A cewarsa, zaman lafiya ya kasance mafi inganci ga kowane irin ci gaba, yana mai jaddada cewa matukar babu zaman lafiya, ba za a samu ci gaba ba a tsakanin al’umma ba.
Ya yaba wa Gwamna Lalong kan kokarinsa na dawo da zaman lafiya da ci gaba, ba ga jihar kadai ba har ma da Arewacin Nijeriya a matsayinsa na shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF).
Injiniya Sule ya ce ya zama dole ya jagoranci wannan ziyara saboda tarihin mutanen jihohin biyu. Ya kara da cewa mutanen Nasarawa ba za su iya jingina hannayensu ba da zarar an samu rikici a Jihar Filato.
Ya kuma roki mutanin jihar da su yi hakuri da junansu ba tare da la’akari da bambancin kabila ko addini ba, musamman cewa babu wani daga cikin manyan manyan addinan biyu da ke yarda da kashe -kashe ko lalata dukiyoyi.
Gwamnan ya yi kira ga mutanen Jihar Filato da kar su yarda ‘yan siyasa su raba dangantakar da ke tsakaninsu ta hanyar cusa gaba da kiyayyan juna a zukatansu.
A nasa jawabin Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya gode wa takwaransa na Jihar Nasarawa da ziyara nuna goyon baya da hadin kai ga gwamnatisa da mutanen Jihar Filato. Ya kara da cewa, Jihar Filato gida ce ga mutanen Jihar Nasarawa. Lalong ya yi godiya ta musamman ga Injiniya Sule kan nuna damuwarsa tun lokacin da rikicin ya barke.