A yau Laraba 7 ga watan Satumba ne gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya rusa majalisar zartarwa ta jiharsa, inda ya sallami dukkan kwamishinoninsa.
Premium Times ta ruwaito cewa, gwamnan ya ce rusa majalisar zartarwar tasa ta fara aiki ne nan take daga ranar ta Laraba.
Batun nasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Babale Yauri.
Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga dukkan kwamishinonin nasa da suka yi aiki tukuru.
Sanarwar ta ce: “Gwamna ya nuna matukar godiya da irin gudumawar da kowane daga cikin kwamishinoninsa ya ba da tare da gode musu bisa ba da lokaci da suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya da ci gaban jihar a lokacin da suke rike da mukamansu.
A bangare guda, ya bayyana cewa, nan ba da jimawa zai sanar da nadin sabbin kwamishinonin da za su maye gurbinsu.
A wani labarin na daban mai bawa babban kwamandan sojojin kasar Iran shawara kan al-amuran tsaro ya bayyana cewa shirin makamai masu linzami na Jumhuriyar Musulunci ta Irana (JMI) ba abin tattaunawa a kai bane.
Majiyar muryar JMI ta nakalto Amir Khatami yana fadar haka, ya kuma kara da cewa tsarin harkokin tsaro na JMI ya ginu ne kan nuna karfi da tsoratar da makiya JMI ne, don haka babu wani abu da zai sa Iran ta amince da tattauna tsarin tsaron kasar ta wata kasa a duniya.
Khatami ya kara da cewa makiya JMI sun fito da ra’ayin tattauna tsarin makamai masu linzami na JMI bayan da suka ga irin ci gaba mai yawa wanda sojojin Iran suka samu a wannan bangaren.
Ya kuma jaddada cewa JMI zata ci gaba da inganta makamanta a dukkan matakan sojojin kasar don tabbatar da cewa makiya sun sai yi tunani mai zurfi kafin su yi kokarin farwa kasar da yaki.
Source: LEGITHAUSA
Source: ABNA