Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya sauke shugaban jami’ar Noma da Kimiyyar Mahalli ta jiharsa daga kan kujerar sa.
A wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar ya fitar, tace gwamnan ya amince da naɗa Farfesa Chiedozie Eze a matsayin mukaddashin VC.
Sanarwan ta yi wa tsohon VC fatan alheri yayin da ta bukaci wanda aka naɗa ya tashi tsaye wajen gina makarantar mai taso wa.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya tsige shugaban jami’ar koyon Noma da Kiwo da Kimiyyar Muhalli ta jihar dake Umuagwo, (VC), Farfesa Patrick Egbule.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Gwamna Uzodinma, ya tunɓuke Farfesan daga kan muƙaminsa ne a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai ranar Laraba a Owerri.
Sanarwan wacce ta fito daga Ofishin Sakataren gwamnatin jihar, Cosmas Iwu, ta ce an maye gurbin Farfesa Egbule da Farfesa Christopher Chiedozie Eze a matsayin mukaddashin VC na jami’ar.
Wani sashin sanarwan ya ce: “Mai girma zaɓaɓɓen gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya amince da sauke Farfesa Patrick Egbule daga kujerar shugaban jami’ar koyon aikin Noma da Kiyo da Kimiyyar Mahalli ta jihar Imo da ke Umuagwo.”
“Bayan haka kamar yadda dokar kafa jami’ar ta tanaza Mai girma gwamna ya amince da naɗin Farfesa Christopher Chiedozie Eze a matsayin shugaban riko na jam’iyyar Noma da Kimiyyar Mahalli ta jiha.”
Gwamna ya yi wa tsohon VC fatan Alheri Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamnan ya yi wa tubabben VC fatan Alheri a dukkanin lamurran da zai fuskanta na gaba, ya kuma gargaɗi sabon ya tashi tsaye.
“Yayin da gwamnan ke wa tsohon muƙaddashin VC fatan Alheri a dukkanin abubuwan rayuwa nan gaba ya kuma buƙaci sabon, Chiedozie Eze, da ya sa kansa ta yadda zai ɗaga darajar makarantar mai taso wa.”
A cewar sanarwa daga gwamnatin jihar Imo.
A wani labarin kuma Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU tace zata ɗauki mataki.
Matukar gwamnatin Buhari ta gaza biyansu Albashin watannin yajin aiki Malaman sun yi baraxanar tsallake zangon karatun da aka yi yajin aiki matukar FG ta kafe kan bakarta na ‘Ba aiki ba albashi’ na waɗannna watannin.
Source:Legithausa