Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya mayar da martani game da kisan Ahmed Gulak, wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress.
Gwamna wike wanda bai yarda da matsayar da gwamna Hope Uzodinma ya dauka a kan batun ba, ya nemi a bar yan sanda su gudanar da bincikensu.
Yayin da ‘yan sanda suka daura alhakin kisan Gulak a kan kungiyar‘ yan aware, Uzodinma ya ce yanayin da ke kewaye da mutuwar dan siyasan ya nuna akasin haka Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ya ce Gwamna Hope Uzodinma yana nuna yanayi kamar cewa ya san halin da ake ciki game da mutuwar Ahmed Gulak ta hanyar bayyana kisan a matsayin kisan siyasa.
Gwamnan na jihar ta Ribas ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, 31 ga Mayu.
Ya nemi takwaran nasa na jihar Imo da ya ba jami’an tsaro damar kammala bincikensu kafin a danganta kisan da aka yi wa jigon na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin kisan siyasa. Wike ya ce ya yi wuri da Uzodinma zai cimma irin wannan matsayar.
Gwamnan na jihar Ribas ya ce: “Bayan aikata hakan, yana nufin cewa ka riga ka san wadanda suka aikata laifin kuma hakan ba zai zama daidai ba. Lokacin da abubuwa irin wannan suka faru, a ba jami’an tsaro damar shiga cikin lamarin sannan su suce duba, daga bincikenmu, wannan shi ne abin da muka gano.”
Gwamna Wike ya tausaya wa iyalan Ahmed Gulak game da kisan dan siyasar.
A gefe guda, kwamishinan yan sandan jihar Imo, Abutu Yaro, yace jami’an hukumar yan sanda sun gano waɗanda suka kashe Ahmed Gulak, fitaccen ɗan siya kuma jigo a APC, kamar yadda Premium times ta ruwaito.
Kwamishinan ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya aike wa hukumar dillancin labarai (NAN) ɗauke da sanya hannun sa ranar Lahadi. Yace Jami’ai sun ɗauki matakin gaggawa bayan samun sahihin bayanai kan maharan, nan danan suka bi sawun su kuma suka gano su.