Gwamna Soludo; Ku ba mu bindigoginku, mun yi alkawarin taimaka muku.
Gwamnan jihar Anambra a yankin kudu maso gabanshin Najeriya ya sanar cewa daga Litinin din wannan makon, an kawo karshen hana jama’ar jihar fita wuraren aiki da sana’o’insu a fadin jihar.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa ta yi ma mutanen da ke dauke da makamai afuwa, musamman wadanda ke yin kira da a raba Najeriya gida biyu kuma a kafa kasa ta ‘yan yankin zalla.
Farfesa Charles Soludo ya sanar da haka cikin wata sanarwa, inda ya jaddada cewa zai dawo da zaman lumana a jihar.
Wasu mayaka, wadanda mambobin kungiyar IPOB ne – kungiyar da gwamnatin Najeriya ta haramta ma aiki a Najeriya – sun rika kai hare-hare a jihar ta Anambra da yankin kudu maso gabashin Najeriya.
Mambobin kungiyar na son a sako shugabansu Mazi Nnamdi Kanu.
READ MORE : An nada Sheikh Nuru Khalid limamin wani masallaci a Abuja.
“Mun yi ma ‘yan uwanmu wadanda ke cikin dazukan jiharmu afuwa. Ku mika mana bindigoginku, kuma ku amince mana mu taimaka muku gina rayuwa mai afani”, inji gwamna Soludo.
READ MORE : Iran A shirye Take Ta Tallafawa Kasar Qatar Wajen Karbar Bakunci Gasar Cin Kofin Duniya.