Gwamna Inuwa na Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya kaddamar da rabon ragar sauro mai dauke da magani kashe sauro na zamani a kokarin kawar da annobar a Jihar Gombe da kasa baki daya.
Gwamnan wanda ya ce har yanzu cutar zazzabin cizon sauro babbar barazana ce ga lafiyar jama’a da walwalar su, duk da haka ya nuna farin ciki kan rahotannin dake nuni da raguwar adadin mace-macen da ake samu daga cutar.
Gwamnan ya bayyana cewa nasarorin da aka samu sun wanzu ne saboda kokarin hadin gwiwa da abokan hulda musamman wadanda suka halarci wajen kaddamarwar.
“An tabbatar cewa amfani da gidan sauro mai maganin kashe kwari da amfani da magungunan rigakafin zazzabin cizon sauro na daya daga cikin ingantattun hanyoyin rigakafin zazzabin cizon sauro masu daurewa.”
Ya ce Gwamnatin Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar gidauniyar tallafi ta duniya za su kaddamar da gangamin guda biyu a hukumance wanda zai nuna fara raba gidajen sauro fiye da miliyan 2 da dubu 300 ga al’ummar jihar gida-gida da Magungunan rigakafin zazzabin cizon sauro a kowane wata zuwa watanni hudu ga yara dake cikin hadari a gundumomi 114 dake kananan Hukumomi 11 na Jihar.