Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya kwanta rashin lafiya ba zai samu zuwa kiran majalisa ba inji mataimakin sa.
Sai dai maimakon haka, Edward Adamu, yace gwamnan zai tura mataimakiyarsa ta wakilce shi ranar Alhamis.
Duk da Alla wadai da sukar da ake masu, majalisar wakilan tarayya ta kafe dole sai CBN ya janye sabon tsarin da ya bullo da shi.
Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ba zai samu zuwa gaban majalisar wakilan tarayya ba a ranar Alhamis, a cewar CBN.
Maimakon haka, mataimkiyar gwamnan CBN a bangaren tsarin daidaita kuɗi, Aisha Ahmad, ce zata wakilce shi wajen amsa gayyatar majalisa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A wasikar baya bayan nan da mataimakin gwamnan CBN na bangaren harkokin haɗaka, Edward Adamu, ya aike wa majalisar wakilan, yace Godwin Emefiele na fama da rashin lafiya.
Ya ce sakamakon wannan rashin lafiya gwamnan ba zai samu halarta da kansa ba amma zai tura wakili.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a ranar Talata 20 ga watan Disamba, 2022 Emefiele ya gaza amsa kiran mambobin majalisa a karo na biyu.
Duk da sukar da suke sha da Allah wadai, ‘yan majalisar wakilan sun sake tsara zuwan gwamnan CBN gabansu ranar Alhamis, sun jaddada kudirin su na ganin bankin ya janye sabon tsarin kayyade cire kuɗi.
Majalisa ta aika wa Emefiele da sammaci ne domin ya zo ya masu ƙarin haske kan sabon tsarin, wanda ya kayyade adadin kuɗin da mutum zai iya cirewa a banki duk mako.
Shin majalisar ta amince gwamnan CBN ya tura wakili? Bayan Femi Gbajabiamila, shugaban majalisa ya karanta wasikar Amadu ga mambobi a tsakiyar zamansu na yau Laraba, yan majalisun sun amince da wakilcin gwamnan babban bankin.
A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya gana da kakakin majalisar wakilan tarayya kan batun sabon tsarin CBN.
A zaman shugabannin biyu sun tattauna kan batun kayyade kuɗin da mutum zai iya cirewa kullum daba banki yadda babban bankin ya bullo da shi.
Hakanan Femi Gabajabimila ya ce sun kuma taɓo abubuwa da dama da ya haɗa da batutuwa da suka danganci babban zaɓen 2023 mai zuwa.