A wata sanarwa wacce babban lauyan dake wakiltar kwamitin lauyoyin Malam Zakzaky, Barista Ishaq Adam ya fitarr wacce kuma aka yada ta a kafafen sada zumunta ta bayyana cewa gobe laraba za’a koma kotu domin cigaba da sauraron wannan shari’a.
Sanarwar ta bayyana cewa, wannan shari’ar za’a cigaba da ita ne a gobe ranar laraba 22 ga watan february na shekarar 2023 a Abuja domin gabatar da tabbataccen saurare.
Amma sanarwar ta nuna cewa, an shirya a fara wannan zama ne tun ranar 3 ga watan na february, 2023 amma hakan bai samu ba, saboda haka aka daga zuwa 22 ga february na shekarar ta 2023.
Sanarwar ta cigaba da nuna damuwa dangane da yadda wannan lamari ya dauki lokaci ake kai ruwa rana wanda hakan bai dace ba.
Hakan ya biyo bayan yanayin da masu kara suke ciki gami da hakkin su na dan adam wanda ke bukatar kada a bata musu lokaci kamar yadda yake a dokance.
Sanarwar ta cigaba da cewa, dadi a kan hakan wannan lamari abin damuwa ne domin masu kara suna bukatar tafiya kasashen ketare domin neman lafiya amma hukumar shige da fice ta ki basu sabbin takardun tafiya (Injternational Passports) wanda yin hakan wani nauyi ne da doka ta dora musu.
Sanarwar ta karkare da addu’ar bayyana gami da cin nasarar gaskiya da kuma kaskantar zalunci da karya.
A karshe sanarwar kuma tayi addu’ar kariya ga Malam Zakzaky da kuma dakin sa Malama Zeenah kuma ta roki Allah ta’ala ya basu lafiya.
A wani labarin na daban kuma matasa almajiran malamin sun gudanar da muzahara a babban birnin Abuja domin kira ga gwamnati tayi kokari ta saki takardun tafiyar malamin dana mai dakin sa domin su samu ‘yancin su na neman lafiya.
An ga matasan mazan su da mata a tinunan Abuja dauke da hoton malamin suna muzaharar lumana gami da kiran a saki takardun jagoran addinin.