An ware ranar 4 ga watan Mayun kowace shekara a matsayin ranar tunawa da jam’ian kashe gobara na duniya, tun biyo bayan iftila’in mutuwar wasu jami’an kashe gobara a wani dajin kasar Austrilia.
An ware wannan rana ne don tunawa da kuma karrama jami’an kashe gobara a fadin duniya kan yadda suke jajircewa tare da sadaukar da rayukansu wajen ceto al’umma da kuma dukiyoyinsu.
Kwanturolan Hukumar Kashe Gobara na Tarayya da ke kula da shiyyar Kano da Jigawa, ACG Ahmad Garba Karaye, wanda ya jagorancin bikin wannan shekarar a Jihar Kano, ya ce wasu daga cikin kyaututtukan da aka ba su, za su kai su asibiti don taimaka wa wanda ke da bukata.
“Ana girmama gwaraza ne a irin wannan rana ne saboda kokarinsu wajen ganin sun kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Ana yin wannan biki ne duk duniya, shi ya sa ake yin sa a ko ina.
“…karfe 12 na rana a duk duniya ana tada jiniya na tsawon minti biyar, wanda ita ake tayar wa idan akwai wani abun gaggawa ko iftila’i da ke bukatar dauki, to haka ake tayar da ita babu abin da ya faru, sai don tunawa mutane da kuma girmama wadannan ma’aikata,” in ji Kwanturolan hukumar a Kano.
Kamar kowace shekara take wannan shekarar shi ne; ‘Martaba Jaruman Da Ke Kare Mu’ wanda ke nuna muhimmancin jami’an hukumar kashe gobara.
A irin wannan rana daidaikun mutane na kai kyaututtuka zuwa ga ofishoshin hukumar kashe gobara da ke kusa da su don karrama su kan yadda suke ceton rayukan mutane.
Shi ma a nasa jawabin, jami’in hulda da jama’a na hukumar, ASF Nura Abdulkadir Maigida, ya ja hankalin jama’a kan muhimmancin bin matakan kariya daga gobara a muhallansu.
Sannan ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumar hadin kai don samun damar yadda za ta wanzar da aikinta cikin sauki.
Daga cikin kayan akwai auduga, bandeji, magunguna da sauran kayan aiki da suka shafi gobara.
A wasu lokutan mutane na kai kyautar kudin don nuna jin dadinsu kan nyadda jami’an hukumar ke taka rawar gani a rayuwar yau da kullum ta al’umma.
Hukumar ta kai ziyara Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda suka duba marasa lafiya da kuma gabatar da kyautar wasu daga cikin kyaututtukan da aka ba su ga asibitin.
Source:LeadershipHausa