Akalla shaguna 40 ne suka kone a wata gobarar dare da ta barke a daren ranar Talata a karamar hukumar Kumbotso da ke jihar Kano.
Shaguna 40 da abin ya shafa na cikin wani katafaren rukunin kasuwanci ne a cikin birnin Kano.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, kimanin shaguna 40 ne a harabar kasuwancin da ke makwabtaka da jerin gidaje na Zawaciki ne gobarar ta kone kurmus.
Wani ganau mai suna Musa Ahmad ya shaida wa manema labarai cewa, shagunan da abin ya shafa sun hada da shagunan sayar da kayayyakin masarufi, shagunan siminti, shagunan PoS, da dai sauransu.
Sai da hukumar kashe gobara ta jihar ta yi amfani da motar ruwa Uku kafin a samu a kashe gobarar.
A wani labarin na daban kungiyoyin ma’aikatan jami’a na SSANU da NASU sun gudanar da zanga-zangar lumana a harabar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jihar Kaduna.
Zanga-zangar dai wani ɓangare ne na yajin aiki da suke gudanarwa kan albashinsu da suka ce gwamnati tarayya ta rike musu na tsawon watanni huɗu a shekarar 2022.
Wakilinmu ya tabbatar da cewa, baya ga zanga-zangar da ma’aikatan suka gudanar a ranar Talata, ma’aikatan sun toshe wasu muhimman kofofin shiga jami’ar da ke Samaru.
Mohammed Yunusa shine shugaban shiyar yayin da yake bayani ga kafafen yada labarai, ya roƙi gwamnati da ta yi gaggawar biyansu albashinsu da sauran buƙatunsu domin gujewa durkushewar ci gaban jami’o’i a kasar baki daya.
“A watan Fabrairu an biya takwarorinmu na ASUU na su bashin amma mu an yi biris da mu”
Dukkan kungiyoyinmu sun yi zanga-zanga kan haka, mun kuma rubuta wasika ga gwamnati domin samun daidaito amma shiru kake ji ya zuwa yanzu.
DUBA NAN: Tinubu Ya Bukaci A Kawo Karshen Matsalar Manoma Da Makiyaya
Yanzu haka, komai ya tsaya cak a cikin jami’ar ba ruwa ba wuta ba karatu dakunan karatun duk a kulle suke.