Gobara ta tashi a tashar mota na NTA da ke Jos, babban birnin Filato a yau Alhamis 24 ga watan Nuwamba.
Jami’an hukumar kashe gobara na tarayya reshen jihar Filato sun isa wurin sun kashe gobarar Maikudi Ibrahim, shugaban tashar ya ce wutar lantarki da aka kawo mai karfi ne ya janyo gobarar da ta janyo asarar dukiyoyi.
Tashar Mota na NTA, shahararren tashar mota a Jos, babban birnin jihar Filato ya yi gobara, Daily Trust ta rahoto. Ba a samu ji ta bakin Mr Mathew Edogbonya, jami’in hulda da jama’a a hukumar kashe gobara ta tarayya na jihar Filato ba.
Wani babban jami’in hukumar, wanda ya nemi a boye sunansa ya tabbatarwa NAN da afkuwar lamarin a Jos.
Jami’in ya ce kawo yanzu ba a gano abin da ya yi sanadin gobarar ba, ya kara da cewa jami’an hukumar sun isa wurin don kashe wutar.
Ya ce: “Jami’in hulda da jama’a na hukumar da wasu sauran jami’ai suna wurin don haka ba zai iya magana ba yanzu.
“Ba za mu iya cewa ga abin da ya yi sanadin wutar ba, amma jami’an mu sun isa wurin don kashe gobarar da takaita asara.
“A halin yanzu, ba za mu iya cewa ga adadin asarar da aka yi ba. Abin da ke gaban mu yanzu shine hana gobarar lalata dukiyoyi ko kashe rayyuka.”
NAN ta rahoto cewa tashar motan yana kallon ginin gidan talabijin na kasa, NTA, Jos da ke kan titin Yakubu Gowon a Jos.
Shugaban tashar ya magantu kan gobarar A bangarensa, Maikudi Ibrahim, shugaban tashar ya shaidawa The Punch a Jos, a ranar Alhamis cewa ba a rasa rai ba amma anyi asarar dukiyoyi, rahoton The Punch.
Ya ce matsalar wutar lantarki ne a yankin da gobarar ya shafa ya yi sanadin afkuwar lamarin.
Kalamansa: “Wutar lantarki mai karfi ne daga Kamfanin Lantarki na Jos ya janyo abin, domin muna tashan, suka kawo wuta, suka dauke nan take.
Hakan ya faru kamar sau goma
Daga nan ne suka kawo karo na 11 sai muka ga tartatsin wuta daga ofishin sakataren kudi kafin mu san abin da ke faruwa wuta ya mamaye ko ina.”
Kano: Gobara ta lakume dukiyoyi na ‘miliyoyin naira’ a Kasunar Singer
A ranar Talata 15 ga watan Nuwamban shekarar 2022, gobara ta tashi a kasuwar Singer da ke jihar Kano.
Gobarar ta tashi ne a wani dajin ajiye kayan masarufi irin su alewa, fulawa, biskit da sauransu a babban kasuwar da ake siyar da kaya kan sari.
Source:Legithausa