Gobara ta tashi a gidan tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da ke unguwar Mundubawa.
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce dakuna shida da suto biyu da dakunan girki biyu da bandakuna sun kome kurmus a gobarar.
Bayan samun nasarar kashe wutar, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta Saminu Yusif Abudullahi, ya ce wutar ta yi barna sosai a gidan.
Jami’in ya ce, “hukumarmu na gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin goabarar, amma mazauna gidan sun alakanta ta da matsalar wutar lantarki.”
Ana zargin gobarar ta daren Lahadi ta fara tashi ne a daga dakin girki sannan ta bazu zuwa wasu sassan gidan, inda aka yi asarar dukiya mai tarin yawa.
A wani labarin na daban mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai bar Abuja zuwa birnin Dallas na kasar Amurka, domin ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a taron kasuwanci na Amurka da Afirka na 2024.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, (NAN), ya ruwaito cewa, hukumar kula da harkokin Afirka ce ta shirya taron.
Mista Stanley Nkwocha, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa a ofishin mataimakin shugaban kasar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Nkwocha ya ce Shettima zai bi sahun sauran shugabannin siyasa da na ‘yan kasuwa a fadin Afirka da Amurka a wajen halartar taron.
A cewarsa, taron zai kunshi tattaunawa kan harkokin kasuwanci da sada zumunta wanda aka shirya gudanarwa a Cibiyar Taro ta Kay Bailey Hutchison a Dallas, Texas.
Ya ce shugabannin Afirka da ake sa ran a taron sun hada da, shugaban kasar, Jamhuriyar Laberiya; Joseph Boakai da shugaban kasar Malawi; Lazarus Chakwera da shugaban kasar Angola, Joao Lourenço.
Nkwocha ya ce, sauran shugabannin Afirka da za su halarci taron sun hada da shugaban kasar Botswana, Mokgweetsi E. K. Masisi da shugaban kasar Cabo Verde, José Maria Neves, da mataimakin firaministan kasar Lesotho, Nthomeng Majara.
Duba Nan: Kwamitin Majalisa Ya Kira Ministan Wuta
Ya ce baya ga zaman taron kolin, Shettima zai yi jawabi a wani taro kan zuba hannun jari a Afirka.