Yan sanda a Kaduna sun kai samame wani sansanin yan bindiga a garin Galadimawa a karamar hukumar Giwa.
DSP MOhammed Jalige, kakakin yan sandan Kaduna ya ce sun yi nasarar kama Yusuf Monore, dan bindiga mai shekara 20 da bindigun AK-47 da harsashi da wayoyi.
Yan sandan sun kuma yi nasarar tarwatsa sansanin yan bindigan bayan musayar wuta da suka yi inda bata garin suka tsere da raunin bindiga.
Yan sanda a Jihar Kaduna sun kama wani dan bindiga mai shekara 20 dauke da bindigu AK-47 guda biyu a garin Galadimawa a karamar hukumar Giwa, rahoton Channels TV.
Kakakin yan sandan Kaduna, DSP Mohammed Jalige, cikin sanarwar da ya fitar ya ce yan sandan Operation Restore Peace ne suka kama shi.
Ya ce yan sandan, bayan samun bayanan sirri, sun kai samame sansanin yan bindiga a dajin Galadimawa suka yi musayar wuta da su.
Yan bindigan, ya ce, sun tsere cikin dajin da raunin harsashin bindiga daban-daban.
A cewar kakakin yan sandan, jami’an sunyi nasarar kama daya cikin yan bindigan, Yusuf Monore, dan shekara 20 dauke da AK-47 guda biyu da harsashi da wayoyin salula.
Jalige ya ce a yanzu ana yi wa wanda ake zargin tambayoyi sannan ana bin sahun sauran da suka tsere, Channels TV ta rahoto.
Kwamishinan yan sanda ya yaba wa jami’an da suka kai samamen.
A bangarensa, kwamishinan yan sandan Jihar, Yekini Ayoku ya jinjinawa dakarun da suka kai samamen sannan ya basu tabbacin cigaba da samun goyon bayansa.
Ya kuma bukaci mazauna Kaduna su cigaba da sanya ido sannan su kai rahoton duk wani abin da ba su gamsu da shi ba wurin hukumomin tsaro.
‘Yn bindiga dai sun addabi kananan hukumomin jihar Kaduna, ko a watannin baya ma wasu masu garkuwa da mutane suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja amma har yanzu jami’an tsaro basu kai ga kwato wadannan fasinjoji ba.
Source:LEGITHAUSA