Hukumar kwallon kafa ta kasar Ghana ta dauki matakin korar kocin tawagar ‘yan kwallon kasar ta Black Stars, Chris Hughton bayan fitar da kasar daga gasar cin kofin Nahiyar Afirka (AFCON) a Cote d’Ivoire.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN), ya ruwaito cewa hukumar kwallon kafar Ghana (GFA) ta sanar da hakan a ranar Talata jim kadan bayan da aka tabbatar da fitar da kasar.
An kori Chris Hughton daga aikinsa na babban kocin tawagar kasar tare da sauran masu taimaka masa nan take.
A wani labarin na daban ana fargabar an kashe mutane da dama tare da kona gine-gine da suka hada da coci-coci da masallatai a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, a wani sabon rikicin addini da ya barke a jihar.
A cewar wani ganau, Pansak Lazarus, wanda dan yankin ne da abin ya shafa, ya shaidawa manema labarai cewa, ba zai iya tantance adadin wadanda suka mutu a halin yanzu ba.
“Ba zan iya ba ku ainihin adadin mutanen da aka kashe ba amma an kashe da yawa, an kona gidaje sama da 15 tare da lalata shaguna da dama,” in ji shi.
Amma jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, wanda ya zanta da manema labarai, ya yi kira da a kwantar da hankula, yana mai cewa, Rundunar ‘yansanda na kan shawo kan lamarin.
Hakazalika, jami’in yada labarai na rundunar soji ta musamman (STF) mai kula da harkokin tsaro a Filato da jihar Bauchi da suka hada da wasu sassan Kudancin Kaduna, mai suna Operation Safe Haven (OPSH), Captain James Oya, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ki yarda ya bayar da adadin wadanda aka kashe.
Source: LEADERSHIPHAUSA