Bayan shafe shekaru 20 yana a majalisar wakilai, shugaban majalisar Femi Gbajabiamila, ya yi murabus daga mukaminsa.
Gbajabiamila, wanda aka rantsar a matsayin dan majalisar a karo na shida a ranar Talata, ya mika takardar murabus dinsa ga sabon kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, a zauren majalisar a ranar Laraba.
A cikin wasikar, shugaban masu rinjaye na majalisar ya ce hakan ne zai ba shi damar rike mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da Bola Tinubu ya ba shi.
A ranar Juma’a, 2 ga watan Yuni, 2023 ne shugaba Tinubu ya nada Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatansa.
An zabe shi a majalisar don wakiltar mazabar tarayya ta Surulere ta 1 da ke Jihar Legas tun a shekarar 2003.
Tsohon dan majalisar ya rike mukamai daban-daban ciki har da mukamin shugaban marasa rinjaye da kuma kakakin majalisar.
Kafin mika takardar murabus din tasa, Gbajbiamila ya gabatar da kudirin farko a zauren majalisa na 10 kan “Bukatar fara daukar matakai don dakile barnar da ambaliyar ruwa ke yi da kuma lalata dukiyoyin jama’a”.
A wani labarin na daban Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba, a ranar Laraba, ya ba da umarnin rufe makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati da ke Jalingo cikin gaggawa sabida tabarbarewar gine-ginen makarantun.
Kefas wanda ya kai ziyarar bazata makarantar da misalin karfe 12:00 na rana, ya kadu matuka game da halin da daliban suke ciki – mummunan halin da azuzun karatu da dakunan kwanan daliban ke ciki.
Gwamnan wanda ya samu rakiyar sakataren gwamnatin jihar, Cif Gibon Kataps; kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Kizito Bonzina, da sauran jami’an gwamnati, ya nuna takaicinsa kan lamarin, ya kuma yi alkawarin gyara makarantar zuwa tsalelen ginin zamani.
Ya kuma ba da umarnin rufe makarantar cikin gaggawa domin gwamnatin ta samu damar fara aikin gyare-gyaren don inganta jin dadin daliban da malamansu.