Wata kyakkyawar budurwa mai amfani da TikTok ta bayyana a bidiyo cewa ta rasa tsayayyen saurayi da zai sota saboda nakasar da Allah yayi mata (Gayu basa kula ta).
Kyakkyawar matashiyar ta ce da zaran namiji ya fito ya ce yana sonta sai ya tsere idan ya gano cewa ita din kurma ce.
Mutane da dama da suka kalli bidiyonta sun karfafa mata gwiwar cewa Ubangiji zai kawo mata wanda zai sota tsakani da Allah .
Wata kyakkyawar matashiyar budurwa mai suna @allthingssimsim, ta je dandalin TikTok don yin bidiyo tare da sanar da mutane dalilin da yasa har yanzu bata da tsayayyen namiji da suke soyayya.
Da take amfani da yaren kurame da rubutaccen kalamai, kyakkyawar budurwar ta bayyana cewa samari na gudunta saboda ita kurma ce.
A karshen dan gajeren bidiyon da tayi, ta kasance dauke da damuwa a fuskarta don nuna halin da take ciki da kuma yadda al’amarin rashin kula ta gayu din keyi gaba daya ya ishe ta.
Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyonta sun shawarceta da dauki kanta a matsayin mai daraja, suna masu cewa wadanda suka ki yin soyayya da ita sune suka yi babban asara ba ita ba.
A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tara ‘likes’ fiye da 100,000 sannan mutum fiye 400 ne suka yi martani Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa: appleuser832939 ya ce: “Yakamata koyon yaran kurame ya zama wajibi ga kowa.”
femm ya yi mamaki: “Ta yaya aka yi kika san sautin da zaki yi amfani da shi.”
Antoine ta ce “Wannan bai da fa’ida…kina da kyau sosai. Kuma gashi nima kurma ce (amma a kunnena na hagu) don haka ya na san abun da ke tattare da haka.” Deshawn Green367 ya ce: “
Me zai hana wannan na nufin zaki iya koyawa gaye abubuwa da yawa.” alwaysjustjohn2 ya ce: “Zamu koyi yaren kurame yau, hakan ba zai hana komai ba. Jayayyanmu zai zamo baki shiru.
Mirchelle Collins ya ce: “Ke kyakkyawa ce ‘yar’uwa ki koya masu yadda zasu yi magana da hannu.”
Source:Legithausa