Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun sace sabon DPO da aka tura karamar hukumar Pankshin ta Jihar Plateau.
Maharan sun bi sabon DPO din da aka tura karamar hukumar kimanin kwana uku da suka shude har dakin hotel dinsa ne suka yi awon gaba da shi.
Majiya daga jami’an yan sanda a jihar ta Plateau ta tabbatar da lamarin tana mai cewa sai da maharan suka harbi DPO din kafin suyi garkuwa dashi.
Yan bindiga sun sace DPO na rundunar yan sanda na Pankshin, a karamar hukumar Pankshin na jihar Plateau, The Punch ta rahoto.
Wani jami’in yan sanda a yankin ya tabbatarwa majiyar Legit.ng Hausa cigaban a Jos, daren ranar Alhamis.
A cewarsa, DPO din, wanda kawo yanzu ba a bayyana sunansa ba, sun sace DPO din ne bayan sun harbe shi a dakinsa na Otel a garin.
Majiyar ta ce: “Kwana uku kenan da turo shi yankin Pankshin.
Yana zaune a wani otel a Pankshin kuma a otel din yan bindigan suka tahp suka harbe shi kafin su yi awon gaba da shi.
Tun lokacin ba mu gan shi ba.”
A lokacin hada wannan rahoton, mai magana da yawun yan sanda na jihar Plateau, DSP Alabo, bai riga ya amsa kira da sakonni da aka tura masa ba.
Wani mazaunin unguwar da aka sace DPO din ya magantu Amma, wani mazaunin unguwar da abin ya faru wanda baya so a bayyana sunansa ya ce an samu karuwar sace mutane a garin a baya-bayan nan kuma kowa na rayuwa cikin tsoro, rahoton Vanguard.
A cewarsa: “Abin ya faru kusa da gidan mu, domin mun gama addu’ar dare kenen sai muka ji karar harbin bindiga.
Mun nemi sanin abin ya da faru an ce wasu yan bindiga ne suka tafi otel din Woktori.
“Da safe ne muka gano cewa masu garkuw ane suka sace sabon DPO da aka tura Pankshin, mun gano cewa mutumin bai dade da zuwa ba kuma ya kama daki a hotel din suka tasho suka sace shi.
”An samu karuwar sace mutane a baya-bayan nan.
Ana zuwa gidajen masu hannu da shuni, za a sace su, sai sun biya kudin fansa kafin a sako su. Wani ma an halaka shi.
Ba a kyale ma’aikatan gwamnatin tarayya ba. Kusan duk sati sai mun ji labari, da zarar ka san kana da kudi, za su zo gidan ka.”
Mahara sun sace tare da yin garkuwa da sabon DPO a Kaduna kan hanyarsa na kama aiki.
A wani rahoton mai kama da wannan, kun ji cewa yan bindiga sun sace sabon DPO na yan sanda da aka tura zuwa Birnin Gwari a Kaduna.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, yana kan hanyarsa na zuwa Birnin Gwari ne don kama aiki.
Source:LegitHausa