A jiya Litinin ne wasu daruruwan fusatattun matasa suka kulle babban titin Gauraka da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a karamar hukumar Tafa cikin jihar Neja, domin gudanar da zanga -zanga kan ci gaba da sace gami da garkuwa da mutane da kuma kai hare –haren ‘yan bindiga a yankin.
Matasan sun dates titin ne da manyan duwatsu, manyan itatuwa, tare da kona tayoyi, inda suka dage kai da fata, babu wani matafiyin da zai wuce ta hanyar har sai gwamnati ta kawo karshen lamarin a yankin.
An ruwaito cewa, masu garkuwar dai, sun jima suna cin karensu babu babbaka a yankin kusan a duk kwanan duniya, inda mazunan yankin ganin sun gaji da aikata masu ta’asar ta yi wa al’ummar yankin dauki dai-dai kuma jami’an tsaro da ke a yankin, sun gaza yin komai na kare lafiyasu da kuma ta dukiyoyinsu, sai suka nuna fushinsu a fili.
Duk da cewa akwai barikin Soji na Zuma a yankin, mazunan yankin sun ba su samun wani daukin gaggawa kan hare–haren da kuma sace jama’arsu, haka nan ba sa samun sukunin yin barci da idanuwan su biyu.
Zanga-zangar dai, ta dakatar da matafiya wucewa ta babban titin.
Bugu da kari, an kuma banka wa wani Caji ofis din ‘yan sanda wuta da ke a yankin.
Idan za a iya tunawa, a watanni biyu da suka gabata anyi garkuwa da mutane bakwai a yankin, inda sai da aka biya kudin fansa Naira miliyan biyu kafin a sako su.
HarIla yau kuma, an sake sace wasu mutane hudu a kwanuka biyar da suka gabata wadanda har zuwa yau ba a sako su ba.
Bugu da kari, gungun wasu masu garkuwa sun kai farmaki a yankin a ranar Lahadi inda suka sace mutane 16.
A wata sabuwa kuwa, an banka wa wata mota wuta da ake zargin masu garkuwa ne a yankin Madalla da misalin karfe 11 na safiyar jiya Litinin.