Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ya yi umurnin rufe wani katafaren kantin siyayya a jihar.
Hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki da masu siyarwa ta rufe kantin ‘Wellcare’ saboda kin karbar tsoffin takardun kudi daga wajen mazauna jihar Gwamnatin jihar Kano ta gargadi yan kasuwa kan cewa za ta dauki tsattsauran mataki kan duk wanda ta kama yana kin karbar tsoffin kudi don bata haramta amfani da su ba.
Gwamnatin jihar Kano ta hannun Hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki da masu siyarwa ta rufe shahararriyar kantin nan mai suna Wellcare, kan kin karbar tsoffin takardun naira a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu.
A cewar mukaddashin shugaban hukumar, Baffa Babba Danagundi, an rufe kantin ne jim kadan bayan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umurnin, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ganduje ya rufe kantin Wellcare Ya ce umurnin rufe kantin ya biyo bayan matakin da kantin Wellcare ya dauka na kin karbar tsoffin takardun Naira daga wajen kwastamomi wanda hakan ya saba umurnin da gwamnatin jihar ta bayar.
Danagundi ya yi gargadi sauran yan kasuwa a Kano da su kwana da sanin cewa gwamnatin jihar bata haramta amfani da tsoffin Naira ba, don haka, duk shagon da aka kama yana kin karbar tsoffin kudin zai fuskanci mummunan hukunci.
Jim kadan bayan rufe kantin ‘Wellcare Alliance Limited’ ya rubuta wasikar ban hakuri zuwa ga gwamnatin inda ya nemi a gaggauta shiga tsakani don sake bude kantin.
Source:LegitHausa