Gwamnatin Jihar Kano ta kori ma’aikatan Hukumar Kula da Harkokin Filaye su huɗu sakamakon sayar da filayen jama’a, amfani da takardun bogi da kuma amfani da jabun bayanai.
Wannan na ƙunshe a wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Muhammad Garba ya fitar a yau Talata.
A sanarwar, Garba ya ce ma’aikatan da a ka kora sun haɗa da Abdulmumin Usman Magami, mai matakin albashi na 06, Abdullahi Nuhu Idris mai matakin albashi na 10, Audu Abba Aliyu mai matakin albashi na 05 da kuma Baba Audu da ke kan matakin albashi na 13.
Garba ya ce an kori ma’aikatan ne bayan rahoton da kwamitin bincike da gwamnati ta kafa ya miƙa sakamakon binciken, bayan ƙorafe-ƙorafe da a ka kai a kan su.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta yi amfani da dokar aiki mai lamba 04406 domin ya zama darasi ga ƴan baya.
Kwamishinan ya yi gargaɗin cewa gwamnati banza ta lamunci aikata laifukan da ga wajen ma’aikatan ta ba.